Rai Bakon Duniya: Gawar Kakakin Gwamna Zulum Za Ta Iso a Yau Lahadi, Za a Yi Jana’izarsa a Abuja

Rai Bakon Duniya: Gawar Kakakin Gwamna Zulum Za Ta Iso a Yau Lahadi, Za a Yi Jana’izarsa a Abuja

  • A yau Lahadi, 14 ga watan Janairu ne ake sa ran gawar kakakin gwamnan jihar Borno, Malam Isa Gusau za ta iso Najeriya daga kasar Indiya
  • Gwamnatin jihar Borno ta sanar da cewar za a sada marigayi Gusau da makwancinsa da misalin karfe 4:00 na yamma a babban birnin tarayya Abuja
  • Za kuma a sallaci gawarsa a babban masallacin Juma'a na Abuja, kamar yadda kwamishinan labarai na jihar Borno ya sanar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Borno - Gwamnatin jihar Borno ta sanar da cewar za a yi jana'izar kakakin gwamnan jihar, Malam Isa Gusau, a yau Lahadi, 14 ga watan Janairu, a babban birnin tarayya Abuja, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

"Kada ku tsinewa shugabanninmu": Sarkin Musulmi ya aika muhimmin sako ga yan Najeriya

A cikin wata sanarwa da ta saki a ranar Asabar, 13 ga watan Janairu, gwamnatin ta bayyana cewa za a yi jana'izarsa da karfe 4:00 na yamma a babban masallacin Juma'a da ke Abuja.

Za a y jana'izar Isa Gusau a yau
Rai Bakon Duniya: Gawar Kakakin Gwamna Zulun Zai Iso a Yau Lahadi, Za a Yi Jana’izarsa a Abuja
Asali: Twitter

Yaushe gawar Gusau zai isa daga Indiya?

Isa Gusau ya rasu ne a ranar Alhamis, a wani asibiti da ke kasar Indiya bayan ya yi fama da rashin lafiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin sanarwar da kwamishinan labarai da harkokin tsaron cikin gida na jihar Borno ya fitar a ranar Asabar, ya bayyana cewa ana sa ran gawar marigayin zai iso Abuja a ranar Lahadi da rana yayin da aka tsayar da birne shi da karfe 4:00 na yamma.

Sanarwar ta kara da cewar gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum zai so kasancewar masu fatan alkhairi a wajen jana'izar da kuma samun addu'o'insu a wannan mawuyacin lokaci.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Mutane sun mutu yayin da motar gwamnati KTSTA ta yi mummunan hatsari, Gwamna ya magantu

Gwamnan ya kuma nuna jin dadinsa da jaje da kuma kalamai masu dadi da al'umma suke ta aikowa kan wannan babban rashi.

Gusau ya yi aiki a matsayin mai bayar da shawara na musamman kan harkokin hulda da jama'a da dabaru ga tsohon gwamnan jihar Borno kuma mataimakin shugaban kasa mai ci, Kashim Shettima.

Ya kasance memba na Cibiyar Hulda da Jama'a ta kasar Birtaniya.

Marigayi Gusau ya rasu ya bar matan aure biyu, yara uku da kanne mata da maza, rahoton Leadrship.

Yan sanda na binciken mutuwar kwamishina

A wani labari na daban, mun ji a baya cewa kwamishinan gyara, sake ginawa da sake matsuguni (RRR) na jihar Borno, Engr. Ibrahim Idris Garba, ya riga mu gidan gaskiya.

Kwamishinan ya rasu ne a safiyar ranar Asabar, 21 ga watan Oktoba, a gidansa da ke rukunin gidajen 777 da ke cikin birnin Maiduguri, babban birnin jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel