Akwai Niyyar Kirki: Abin Da Ya Sa Zan Taimaki Gwamnatin Abba, Aliko Dangote

Akwai Niyyar Kirki: Abin Da Ya Sa Zan Taimaki Gwamnatin Abba, Aliko Dangote

  • Abba Kabir Yusuf ya roki masu kudin da suka fito daga Kano su bada gudumuwarsu a halin da ake ciki
  • Aliko Dangote ya kawo ziyara gidan gwamnati, ya dauki alkawari zai taimaka wajen kawo cigaba a mahaifarsa
  • Shugaban kamfanin Dangote Group ya ce kyakkyawar manufar Gwamna Abba ta jawo shi jihar Kano ba komai ba

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - A ranar Juma’a, Abba Kabir Yusuf da mukarrabansa suka karbi bakuncin Aliko Dangote a gidan gwamnatin jihar Kano.

Mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da haka a shafin X, ya yi farin ciki da mai kudin nahiyar Afrikan ya waiwayi gida.

Dangote
Aliko Dangote da Abba Kabir Yusuf a Kano Hoto: @KYusufAbba
Asali: Twitter

A jawabin da ya gabatar, ‘dan kasuwan ya ce a bude kofarsa ta ke wajen ganin ya bada gudumuwa domin cigaban mutanen Kano.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya faɗi hanyar da mutane zasu bi su Kare kansu daga hare-haren ƴan bindiga

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aliko Dangote ya yi alwashi zai taka rawar gani domin kawo cigaba musamman la’akari da yadda Kano tayi zarra a duk Arewa.

Duk matsalar tsaron da ake fama da ita, Dangote ya ce Kano ta tsira don haka ‘dan kasuwa ba zai ji kyashin narka dukiya a jihar ba.

Hadimin gwamnan Kano, Abdullahi Ibrahim ya wallafa jawabin Aliko Dangote a X. Kano da Kanawa suna alfahari da 'dan na su.

Meyasa Dangote zai taimakawa Abba a Kano?

"Ina so in tabbatar maka za mu bada gudumuwa, ba saboda kurum daga jihar Kano na fito ba, saboda ka na da niyya mai kyau."
"Ka na da goyon bayan al’umma. Za mu cigaba da goyon bayanka da gwamnatinka."

- Aliko Dangote

Yadda Dangote zai bada gudumuwa a Kano

Vanguard ta ce mai kudin Afrikan zai taimaka domin magance matsalolin kiwon lafiya da ilmi, kuma ya taimakawa marasa karfi.

Kara karanta wannan

APC tayi maganar yunkurin dawo da Sanusi II gidan sarauta da rushe masarautun Kano

Gwamna Abba ya yi alkawarin yin ayyuka asibitin Murtala Muhammad, kuma zai kafa asibiti na musamman ta masu cutar sikila.

Baya ga nuna ana tare, Alhaji Dangote ya bada hakurin yadda ya kawo ziyara a gajeren lokaci, ya bada uzurin tafiye-tafiye yake yi.

Kiran Gwamnatin Abba ga su Dangote

A makon nan Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga attajiran jihar su kawowa al’umma agaji, Dangote ya ce a shirye yake da ya taimaka.

Mai girma gwamnan ya nuna takaicinsa game da yadda kaya suka tashi a kasuwa, yake cewa akwai bukatar a saukaka Kanawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng