Yadda masana kiwon lafiya suka fara magance cutar sikila a jikin dan Adam

Yadda masana kiwon lafiya suka fara magance cutar sikila a jikin dan Adam

- Kwayoyin cutar sikila ko amosanin jini, suna daya daaga cikin cututtuka da ke daidaita rayuwar dan Adam

- Mafi akasarin hanyar daukan wannan cuta shine tsakanin ma'aurata masu rukunin jini na AS ko SS da suka yi aure ba tare da gwaji ba

A wani bincike na masana kiwon lafiya, sun bayyana cewa Najeriya tana daya daga cikin kasashen da su ka fi yawan mutane ma su dauke da wannan cuta.

Sun bayyana cewa ana alakanta wannan cuta ne da rashin gwaji na jini tsakanin ma'aurata kafin su yi aure.

Wannan cuta tana matukar daidaita rayuwar ma su ita, wadda mafi yawancinsu sun fitar da rai, sun cewa mutuwa dai yau ko gobe.

Yadda masana kiwon lafiya suka fara magance cutar sikila a jikin dan Adam
Yadda masana kiwon lafiya suka fara magance cutar sikila a jikin dan Adam

Rahotannin daga shafiin BBC, sun bayyana yadda wasu mata guda biyu suka samu waraka daga wannan cuta da su ka sha fama da ita tun su na 'yan jarirai.

Wannan mata Halima da Samira, sun bayyana yadda mahaifinsu ya sha fama wajen nema mu su magani a kasashe daban daban a fadin duniyar nan.

KU KARANTA: Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a musulunci

A cikin wannan yawon neman maganin ne, aka yi sa'a a kasar Austria, inda likitoci su ka debi bargon wani dan uwansu wanda ba shi da wannan cuta, suka zuba musu a jikinsu, wanda wannan kadai shine sanadiyar karshen wannan wahala ta su.

Sun yi farin cikin da godiya ga Madaukakin Sarki, sai dai sun bayyana cewa sun kashe kimanin kudi Naira miliyan 25 ga kowanensu.

Don shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a :labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukan mu na a:

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel