Rashin Tsaro: Gwamnan Arewa Ya Nada Tsohon Sifetan ’Yan Sandan Najeriya Shirgegen Mukami a Jiharsa

Rashin Tsaro: Gwamnan Arewa Ya Nada Tsohon Sifetan ’Yan Sandan Najeriya Shirgegen Mukami a Jiharsa

  • Tsohon sifetan ‘yan sandan Najeriya, Mohammed Abubakar ya samu babban mukami a gwamnatin jihar Zamfara
  • Gwamna Dauda Lawal Dare ya nada tsohon sifetan ‘yan sandan Najeriya mukamin shugaban kwamitin asusun tsaro a jihar
  • Kakakin gwamnan, Suleiman Idris shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a birnin Gusau a jiya Laraba 7 ga watan Faburairu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Zamfara – Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare ya nada tsohon sifetan ‘yan sandan Najeriya mukami.

Dare ya nada Mohammed Abubakar a matsayin shugaban sabuwar hukumar asusun tsaro a jihar, cewar TVC News.

Gwamna Dare ya nada tsohon sifetan ’yan sandan Najeriya mukami
Gwamnan Dauda Lawal Ya Nada Tsohon Sifetan ’Yan Sandan Najeriya Mukami. Hoto: Dauda Lawal, MD Abubakar.
Asali: Facebook

Wane mukami aka naɗa MD Abubakar?

Yayin jawabin kaddamar da mambobin kwamitin a jiya Laraba 7 ga watan Faburairu, gwamnan ya bayyana himmatuwarsa kan tsaro a jihar.

Kara karanta wannan

Mahara sun sake hallaka fitaccen basarake a jihar Arewa, bayanai sun fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya ce a shirye ya ke don dakile dukkan matsalolin tsaron jihar da suka hada da garkuwa da mutane da fashin daji.

Kakakin gwamnan, Suleiman Idris shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a birnin Gusau.

Idris ya ce an samar da kwamitin ne don tara kudade saboda taimakon gwamnatin jihar wurin dakile matsalar tsaro, cewar Daily Nigerian.

Bukatar Gwamna Dare ga mambobin kwamitin

Gwamnan ya bukaci mambobin kwamitin da su samar da kudade don taimakawa gwamnatin dakile matsalar da ta addabe su.

Ya ce:

“An yanke shawarar kirkirar kwamitin ganin yadda matsalar tsaro ke kara kamari a jihar da kuma matsalolin da ke tare da hakan.
“Hakan ya zamo barazana ba iya ga gwamnatin Zamfara ba kadai har ma kasar baki daya.
“Shekaru da dama, matsalar tsaron ta jawo asarar dubban rayukan jama’a da kuma asarar dukiyoyin al’umma.”

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Gwamnan arewa ya ayyana hutun kwana 1 a jiharsa, ya kawo dalili mai ƙarfi

Har ila yau, gwamnan ya ce matsalar ta durkusar da karfin tattalin arzikin jihar musamman harkar noma da ilimi da lafiya da kuma kasuwanci.

Zulum zai karya farashin fetur ga Manoma

Kun ji cewa Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya shirya karya farashin fetur don taimakawa manoma a jihar.

Zulum ya yi alkawarin hakan musamman ga manoman Damasak a jihar don saukaka musu wahalhalun tsadar fetur.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.