Allahu Akbar: Shahararren Ɗan Jaridar Wasanni, Kayode Tijani, Ya Kwanta Dama
- Rahotanni na nuni da cewa Allah ya karbi rayuwar shahararren dan jarida a fannin wasanni, Kayode Tijani a asibitin Legas
- Kayode Tijani ya rasu yana da shekaru 55 bayan fama da rashin lafiya, kuma ya bar mata daya da 'ya'ya da dama
- Tijani ya shahara a dauko Labarin wasanni, kuma ya taba rike daraktan yada labarai na tsohon ministan wasanni, marigayi Akinyele
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Legas - A jiya ne masoya harkokin wasanni a Najeriya suka shiga cikin makoki yayin da wani fitaccen dan jaridan wasanni Kayode Tijani ya rasu.
Tijjani ya rasu jiya a asibitin koyarwa na jami’ar jihar Legas (LASUTH), Ikeja bayan ya sha fama da jinya.
Yau Alhamis za ayi jana'izar Tijani
An tabbatar da mutuwar Tijjani ta hannun ‘yar uwarsa, Dokta Ganiyat Tijani-Adenle, babbar malama a jami’ar jihar Legas (LASU).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dokta Tijani-Adenle ta shaida wa jaridar The Nation cewa za a yi jana'izarsa a yau (Alhamis) a makabartar Atan (bangaren Musulmai), Yaba, Legas da karfe 2 na rana.
Tijjani mai shekaru 55 ya rasu ya bar mata daya da ‘ya’ya da dama.
Shaharar da Tijani yayi a harkar wasanni
Marigayi Tijjani shi ne babban jami'in gudanarwa na SportsXclusive da Sports Focus International.
Ya fara aikin jarida tun yana karami, kuma ya samu damar zama daya daga cikin fitattun manazarta wasanni a Najeriya.
Ya taba zama babban sakataren yada labarai na marigayi tsohon ministan wasanni, Cif Alex Akinyele.
Marigayi Tijjani, wanda ya fara aikin jarida a fannin wasanni a shekarar 1987, ya je wurare masu nisa domin dauko labaran wasanni a fadin duniya.
Sarki Joseph Edozien na masarautar Asaba ya kwanta dama
Babban basarake lamba daya a Asaba, babban birnin jihar Delta, Joseph Edozien ya kwanta dama.
An ruwaito cewa mai martaba Sarki Edozien ya rasu ne a jiya Laraba, duk da cewa har yanzu masarautar ba ta fitar da sanarwa kan mutuwar ba.
Edozien shi ne Sarkin Asaba na 13, kuma yana cikin shirye-shiryen bikin cika shekara 100 ne wa'adinsa a duniya ya kare.
Asali: Legit.ng