Dalilin da Yasa Har Yanzu Ba a Rantsar da Sabbin Alkalan Kotun Koli Ba Kwanaki 48 Bayan Tantance Su
- Bayan sama da kwanaki 45 da majalisar dattawa ta tantance su, an gano dalilin da ya sa ba a rantsar da sabbin alkalan Kotun Koli ba
- Alkalan, su 11 an kara masu matsayi daga Kotun Daukaka Kara zuwa Kotun Koli a ranar 21 ga watan Disamba 2023
- Daga cikin dalilan da yasa ba a rantsar da su ba, akwai rashin gida da mota da kuma rashin karasa shari'o'in da ke gabansu a Kotun Daukaka Kara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
An samu wasu bayanan sirri kan dalilin da ya sa aka samu tsaiko wajen rantsar da sabbin alkalan Kotun Koli su 11 da majalisar dattawa ta tantance su a watan Disamba.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wasu daga cikin dalilan sun shafi rashin gidan zama da sufurin kayan alkalan.
Jerin sunayen sabbin alkalan Kotun Koli su 11
Majalisar dattawan a ranar 21 ga watan Disamba, 2023, ta tantance Haruna Tsammani (Arewa maso Gabas); Moore Adumein (Kudu maso Kudu); daJummai Sankey (Arewa ta tsakiya).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran sun hada da Chidiebere Uwa (Kudu maso Gabas), Chioma Nwosu-Iheme (Kudu maso Gabas), Obande Ogbuinya (Kudu maso Gabas) da Stephen Adah (Arewa ta tsakiya).
Ragowar su ne Habeeb Abiru (Kudu maso Yamma); Jamilu Tukur (Arewa maso Yamma); Abubakar Umar (Arewa maso Yamma) da Mohammed Idris (Arewa ta tsakiya).
Dalilan da yasa har yanzu ba a rantsar da alkalan ba
Wani ma'aikaci a hukumar shari'a ta tarayya (FJSC) wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce wasu dalilan sun hada da rashin karasa shari'o'in da suka fara a Kotun Daukaka Kara.
Da yake magana akan tsaikon da aka samu, wani babban lauya, Murtala Abdulrasheed ya ce ba a samar da isassun kudi don kawata gidaje, ofis ofis da sayen motocin sabbin alkalan ba.
Wani ma'aikaci a Kotun Koli wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da cewa har yanzu ba a sayi motocin sabbin alkalan ba, kuka kowanne alkali zai samu mota uku.
Ya kara da cewa akwai korafi da aka shigar akan wani alkali daya amma yanzu an warware matsalar.
Sai dai duk wani yunkuri ta jin ta bakin daraktan watsa labarai na Kotun Koli, Dr. Festus Akande ya ci tura.
An bankado badakalar naira biliyan 12 a Kotun Koli
Wani bincike da ofishin Odita-Janar na Tarayya (OAuGF) ya gudanar ya nuna cewa an karkatar da naira biliyan 12 daga asusun Kotun Koli daga 2017 zuwa 2021.
Haka zalika rahoton binciken ya nuna cewa akwai wasu kadadori da suka hada da filaye mallakin kotun da aka cefanar da su.
Asali: Legit.ng