Jerin Sabbin Alkalan kotun daukaka kara da CJN Tanko ya rantsar ranar Litinin
Shugaban Alkalan Najeriya CJN Tanko Muhammad, ya rantsar da Alkalai 18 da aka karawa girma zuwa kotun daukaka kara.
na jerin sabbin Alkalan kotun daukaka kara da TheNation ta jero:
Yankin Arewa maso tsakiya
1. Mohammed Danjuma (Niger)
2. Muhammad Sirajo (Plateau)
Yankin Arewa maso gabas
3. Abdul-Azeez Waziri (Adamawa)
4. Yusuf Bashir (Taraba)
5. Usman Musale (Yobe)
6. Ibrahim Jauro (Yobe)
Yankin Arewa maso yamma
7. Abba Mohammed (Kano)
8. Bature Gafai (Katsina)
9. Danlami Senchi (Kebbi)
10. Mohammed Abubakar (Sokoto)
11. Hassan Sule (Zamfara)
DUBA NAN: Danbarwa Ta Ɓarke a Jam'iyyar APC Bayan Sanar da Ɗan Takarar Gwamna a Zaɓen Dake Tafe
KU KARANTA: Jagoran APC a Zamfara, AbdulAziz Yari, ya yi tsokaci kan komawar Matawalle APC
Yankin kudu maso gabas
12. Kenneth Amadi (Imo)
Yankin kudu maso kudu
13. Peter Affen (Bayelsa)
14. Sybil Gbagi (Delta)
Yankin kudu maso yamma
15. Olasunbo Goodluck (Lagos)
16. Adebukola Banjoko (Ogun)
17. Olabode Adegbehingbe (Ondo)
18. Bola Ademola (Ondo)
A jerin Alkalai, 11 daga cikin sun fito ne daga yankin Arewa yayinda 7 suka so daga kudu.
An nada Alkalan Shari'a 34 a jihar Kano bayan gwaji
A bangare guda, da amincewar Mai Shari’a Nura Sagir, babban alkalin Kano, an kara wasu alkalai 34 na kotun shari’ar Musulunci a jihar a ranar Alhamis, 24 ga watan Yuni.
Kakakin ma’aikatar shari’ar jihar, Baba Jibo-Ibrahim ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, jaridar Punch ta ruwaito.
Jibo-Ibrahim a cikin wata sanarwa ya bayyana cewa Babban Alkalin ya amince da nadin alkalan ne bayan sun ci jarabawar da Hukumar Kula Harkokin Shari’a ta Kasa (NJC) ta gudanar.
Asali: Legit.ng