Ayyiriri: Kotun Koli Za Ta Yi Sabbin Angwaye, NJC Ta Amince da Nadin Alkalai 11

Ayyiriri: Kotun Koli Za Ta Yi Sabbin Angwaye, NJC Ta Amince da Nadin Alkalai 11

 • Majalisar shari'a ta Najeria (NJC) ta amince da karin matsayin alkalai 11 daga Kotun Daukaka Kara zuwa Kotun Koli
 • NJC ta ce majalisar ta dauki wannan matakin ne a taronta na 104 bayan duba jerin sunayen da kwamitinta ya mika mata
 • Babban joji na kasa (CJN), Olukayode Ariwoola ne ya jagoranci zaman wanda kuma shi ne shugaban majalisar NJC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

FCT, Abuja - Majalisar shari'a ta Najeria (NJC) ta amince da karin matsayi ga masu shari'a 11 daga Kotun Daukaka Kara zuwa Kotun Koli.

Majalisar NJC ta dauki wannan mataki ne a taron da ta gudanar a ranar Laraba, 6 ga watan Disamba, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yayin da ake dakon hukuncin Kotun Koli, Hukumar NJC ta yi abu 1 don inganta bangaren shari'a

Kotin Koli/Kotun Kolin Najeriya/Kotun Daukaka Kara
Majalisar shari'a ta Najeriya na da karfin ikon nadawa tare da hukunta duk wani ma'aikacin shari'a. Hoto: Aso Rock Villa
Asali: UGC

Babban mai shari'a na kasa (CJN), Olukayode Ariwoola ne ya jagoranci zaman wanda kuma shi ne shugaban majalisar NJC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NJC ta amince da nadin sabbin alkalan Kotun Koli

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan watsa labarai na majalisar, Soji Oye.

Kamar yadda rahoton The Nation ya nuna, Oye ya ce za a rantsar da sabbin alkalan Kotun Koli idan shugaban kasa Bola Tinubu da majalisar dattawa sun amince tare da tabbatar da nadin nasu.

Jaridar Legit ta gano cewa taron da majalisar ta gudanar a ranar Laraba shi ne zamanta na karshe a wannan shekarar ta 2023.

Wadanda majalisar ta amince da karin matsayin su sun hada da:

 1. Mai shari'a Jummai Hannatu Sankey
 2. Mai shari'a Chidiebere Nwaoma Uwa
 3. Mai shari'a Chioma Egondu Nwosu-Iheme
 4. Mai shari'a Haruna Simon Tsammani
 5. Mai shari'a Moore Aseimo A. Adumein
 6. Mai shari'a Obande Festus Ogbuinya
 7. Mai shari'a Stephen Jonah Adah
 8. Mai shari'a Habeeb Adewale O. Abiru
 9. Mai shari'a Jamilu Yammama Tukur
 10. Mai shari'a Abubakar Sadiq Umar
 11. Mai shari'a Mohammed Baba Idris

Kara karanta wannan

Ku zo ku siya: An saka jirgin shugaban Najeriya a kasuwa, ana neman mai saye

Haka zalika, NJC ta amince da nadin mai shari'a Mohammed Ramat zuwa Kotun Daukaka, da kuma nadin wasu shugabannin kotuna shida da jami'an shari'a 26.

An nemi Kotun Koli ta tsige Shugaba Tinubu

A wani labarin na daban, Legit Hausa ta ruwaito maku cewa jam'iyyar Hope Democratic Party (HDP) ta nemi Kotun Koli ta tsige Shugaba Tinubu.

Jam'iyyar HDP da dan takarar shugaban kasar ta a zaben 2019, Ambrose Owuru, sun ce Tinubu ya karbi ragamar shugabancin kasar ba bisa ka'ida ba.

Ta ce Tinubu na sane da cewa akwai shari'ar da ake yi kan sa a Kotun Koli kan yadda aka gudanar da zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel