Hukumar EFCC Ta Kirkiri Dakarun Mutum 7000 da Za Su Yaki Masu Tashin Farashin Dala
- Hukumar EFCC za ta tashi tsaye, ta yaki wadanda su ke bada gudumuwa wajen karya darajar Naira
- Yayin da kudin Najeriya ta ke rasa darajarta a kasuwa, farashin Dalar Amurka yana tashi har gobe
- Dakarun EFCC na musamman sun soma cafke masu cin mutuncin Naira da karbar Daloli babu dalili
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - A kokarin ganin an yi maganin mummunan karyewar Naira da tashin Dala, hukumar EFCC tayi wani hobbasa a Najeriya.
EFCC mai yaki da rashin gaskiya ta fitar da jawabi a shafinta, ta kafa wata runduna ta musamman saboda masu jawo tashin Dala.
A halin yanzu babu abin da Naira ta ke yi sai rasa daraja da kima a kan Dalar kasar Amurka, har su Ben Bruce sun kawo shawarwari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai magana da yawun bakin hukumar EFCC a kasa, Dele Oyewale ya shaida cewa ana neman ganin yadda za a rage sululun Naira.
CBN da EFCC sun hada kai
Saboda a kawo mafitar tattalin arziki, Punch ta ce ministan kudi watau Wale Edun ya yi zama da shugaban EFCC da gwamnan CBN.
Ma’aikatar tattalin arziki ta tabbatar da zaman Ola Olukoyede da Olayemi Cardoso a shafin X.
A karshen zaman sai aka cin ma matsaya cewa bankuna za su saida ragowar dalolin da ke asusunsu domin a rage adadin mabukata.
EFCC za ta iya hana Dala tashi?
EFCC ta ce an zakulo jami’ai na musamman daga kowace shiyya domin samar da rundunar da za tayi maganin matsalolin kudi.
Hukumar ta ce aikin rundunar ita ce yakar masu wulakanta Naira da masu jawo Dala ta tashi, hakan zai ceto tattalin arzikin Najeriya.
Ola Olukoyede yake cewa toshe duk wata kafa zai hana a rika wasa da hankalin jama’a wanda tuni an fara yin kame a garuruwa.
Me ya jawo Dala ta tashi sosai?
Da Gwamnan bankin CBN ya je gaban ‘yan majalisa, an ji labari ya fada masu yawan fita makarantu da asibitocin ketare ya karya Naira.
Baya ga rububin kudin Amurkan da ake yi, Yemi Cordoso ya ce ba a samu dalolin sosai daga cikin danyen man Najeriya a kasar waje.
Asali: Legit.ng