Za a Zauna: Kwankwaso Ya Aikawa Sarakunan Kano Sako Kwanaki da Nasarar Kotun Koli

Za a Zauna: Kwankwaso Ya Aikawa Sarakunan Kano Sako Kwanaki da Nasarar Kotun Koli

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya yi hira da manema labarai daga isowansa garin Kano a tsakiyar makon nan
  • Babban ‘dan siyasar ya tofa albarkacin bakinsa a game da masarautun da gwamnatin APC ta kirkiro
  • Kwankwaso yana ganin nan gaba dole gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta zauna a game da wannan batu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Rabiu Musa Kwankwaso ya yi doguwar hira da manema labarai a ranar Alhamis, 18 ga watan Junairu 2023 a Kano.

Tashar rediyon Nasara FM tana cikin wadanda suka dauko hirar kai-tsaye da aka yi da jagora kuma ‘dan takaran na NNPP a 2023.

Sarakunan Kano
Kwankwaso ya yi maganar Sarakunan Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

A tattaunawar da aka yi da shi, Rabiu Musa Kwankwaso ya tabo batun masaratun da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta kafa.

Kara karanta wannan

Lauya Mazaunin Kano Ya Magantu Kan Yadda Gwamna Abba Yusuf Zai Mayar Da Sanusi Kan Gadon Sarauta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso, Abba da masarautun Kano

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa ba a taba yin zama da shi domin tattauna makomar masarautun ba, amma ya ce ya san za ayi.

Rabiu Kwankwaso ya nuna gwamnatin Abba Kabir Yusuf da NNPP za ta dauki matakin da ya dace a game da sababbin masarautun.

Kwankwaso ya ce tarko aka shirya da masarautu

Legit Hausa ta bibiyi hirar da aka yi da magudun darikar ta Kwankwasiyya, mun ji yana zargin gwamnatin da ta wuce da mugun nufi.

Duk da haka, Sanata Kwankwaso ya ce wani lokacin a kan iya kawo mugun tsari amma ya amfanar ko kuwa a ci karo da akasin haka.

‘Dan takaran shugaban kasar na zaben 2023 yake cewa tarko aka shirya wajen kirkiro sarakuna a Rano, Bichi, Gaya da kuma Karaye.

Ibrahim Adam ya tsakuro bangaren wannan zance ya wallafa a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

"Kofar NNPP a bude take ga masu son yin maja", Kwankwaso

Kano: Muhammadu Sanusi II zai dawo?

Kwankwaso ya shaidawa ‘yan jarida cewa gwamnatin jihar Kano za ta ga abin da ya fi dacewa tsakanin gyara ko kuwa rusa masarautun.

Ana ta rade-radin gwamnatin NNPP mai-ci za ta maido Muhammadu Sanusi II.

Tsohon sanatan na tsakiyar Kano bai bayyana matakin da za a dauka ba, amma ya nuna za ayi abin da zai fi zama alheri ga al’umma.

Abin da Rabiu Kwankwaso ya fada

“Amma na san dole za a zo ayi magana, a ga menene ya kamata a yi, ta ina za a bullo.
"Ya za ayi? Haka za a bari? Gyara za ayi? Rusau za ayi? Za a zo a duba. Abin da ya kamata ayi, shi za ayi."

- Rabiu Musa Kwankwaso

Kotun koli: Sanusi II ya yi magana

Ana da labari cewa Muhammadu Sanusi II ya soki tawakkalin Nasiru Gawuna, ya zargi APC da kokarin karbe mulki da karfin tsiya.

Khalifa ya ce APC ta makara wajen karbar kaddara tun da sai da aka jira kotun koli ta yanke hukunci karshe a kan takarar Kano a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel