Girman Rawani Na Ya Fi Karfin Yan Bindiga Su Sace Ni Ko Hallaka Ni, Fitaccen Basarake Ya Yi Alfahari
- Fitaccen mai sarautar gargajiya, Oba Abdulrasheed Akanbi na Iwo ya yi alfahari kan 'yan bindiga
- Basaraken ya ce girman rawaninsa ya fi karfin wani dan bindiga da aka haifa ya kai masa farmaki a yanzu
- Wannan na zuwa ne bayan 'yan bindiga sun hallaka manyan sarakunan gargajiya uku a jihar Ekiti
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Osun - Oba Abdulrasheed Akanbi na Iwo ya yi alfahari kan sace-sacen da 'yan bindiga ke yi.
Basaraken ya ce girman rawaninsa ya fi karfin 'yan bindiga su sace shi ko kuma hallaka shi a Najeriya.
Mene basaraken ke cewa kan 'yan bindiga?
Oluwo ya ce Ubangiji ya zabe shi kuma ya kare shi daga dukkan irin wasu sharruka da za su same shi, cewar The Nation.
Yadda jami’an yan sanda suka yi garkuwa da wani mazaunin Abuja, suka kwashe gaba daya kudin asusunsa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce ya riga ya tsare kansa ta yadda babu yadda za a yi wani mai sharri ya yi galaba a kansa ko sarautarsa.
Akanbi ya bayyana haka ne yayin hira da 'yan jaridu a fadarsa a yau Laraba 7 ga wata Faburairu, cewar Linda Ikeji.
Sarkin na Iwo na magana ne kan kisan masu sarautar gargajiya 2 a jihar Ekiti da kuma daya a jihar Kwara a makon da ya gabata.
Ya ce:
"Babu wani mai garkuwa da mutane da ya isa ya kai min hari ko hallaka ni a wannan duniya.
"Za su iya gwadawa kuma za su dandana karfin mulkin da nake tare da shi da girman rawani na.
"Ubangiji ne ya ke rike da masarautu, ba za su iya kashe ni ko sace ni ba, idan ka sake Allah dole za ka samu damuwa."
Mene basaraken ya ce kan masu sarauta?
Ya ce yanzu sarakuna duk sun dawo bayin gwamnati inda ya yi Allah wadai da irin rashin tsaro da ake fama da shi a yankin Yarbawa.
Ya kara da cewa:
"Babu wani mai garkuwa ko dan fashi da aka haife shi da zai iya kai min hari a wannan yanayin.
"Abin takaici ne yadda rashin tsaro ya yi yawa a yankin Yarbawa, ana cire sarakuna lokacin da aka ga dama, sun zama bayin gwamnati, hakan abin kunya ne."
Mahara sun hallaka sarakuna 3
Kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun kai farmaki kan wasu sarakunan gargajiya 3 a jihar Ekiti.
Maharan sun yi nasarar hallaka 2 daga cikinsu yayin da daya basaraken ya tsira da kyar daga harin.
Asali: Legit.ng