Sanata Ya Fadakar da Mutane a Kan Hanyoyi 3 da Za a Bi Domin Karya Dalar Amurka
- Ben Murray Bruce yana goyon bayan #BuyNaijaToGrowTheNaira da gwamnatin tarayya ta kawo
- Ana neman jama’a su nuna kishin kasa wajen sayen kaya, wannan zai sa a rage dogaro da Dala
- Sanata Ben Bruce ya bada shawara a rika yi wa kamfanonin Glo, Innoson da kuma Dangote ciki
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Ben Murray Bruce ya bi sahun masu fashin baki, su na tofa albarkacin bakinsu game da halin tattalin arzikin da ake ciki.
Sanata Ben Murray Bruce yana ganin dole sai an karfafi kamfanonin gida idan dai ana so darajar Naira ta tashi har Dala ta iya sauki.
Fitaccen ‘dan kasuwa kuma ‘dan siyasar yake cewa muddin aka yi watsi shawararsa, wata rana za ayi gari $1 ta kai N5,000 a kasuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar tsohon Sanatan na Bayelsa, yadda za a bi wajen gyara tattalin arziki ba abu ne mai wahala kamar yadda wasu ke tunani ba.
Tattalin arziki: Shawarar Ben Murray Bruce
"Idan mu a matsayinmu na ‘yan Najeriya muna so Naira tayi kima, dole mu yi wadannan abubuwa ba tare da bata lokaci ba:"
"Mu yi amfani da Glo domin kiran waya da hawa yanar gizo."
"Mu ci kayan Dangote domin samun sinadarai da karfi."
"Mu tuka Innoson domin ganin Najeriya tayi sauri."
"Idan ba mu yi wadannan abubuwa uku ba, sai mu zo ana ba’a a dandalin sada zumunta, wata rana za a ji $1 za ta N5000."
- Ben Murray Bruce
Tun a shafinsa na X da ya yi wannan magana wasu su ka rika maida masa martani cewa ba da motocin kirar Innoson yake amfani ba.
Ta ya Dala za ta sauka a kan Naira?
Kalu Aja wanda masanin tattalin arziki ne ya ankarar da tsohon Sanatan na PDP irin raunin da ke tattare da shawarwarin da ya kawo.
Mista Kalu Aja ya ce kamfanin Glo yana sayo na’urorinsa ne daga kasar waje haka zalika Aliko Dangote ya kan kawo hatsi daga ketare.
Idan ana so Naira ta kara Daraja, Aja yana ganin sai Najeriya tana fita da kayanta zuwa kasashen waje domin Daloli su rika shigowa.
Wahalar tattali ta jawo zanga-zanga
Ana da labari shugaban kasar Najeriya ya bada umarni daga Faransa a magance matsalar abinci da mutane suka fara zanga-zanga.
Jam'iyyar APC tana zargin 'yan adawa suna da hannu a zanga-zangar da aka shirya a makon nan saboda yadda rayuwa tayi kunci a kasa.
Asali: Legit.ng