Albishirin ku: Gobe masu layin GLO za su ci banza

Albishirin ku: Gobe masu layin GLO za su ci banza

- Globacom za su bada goron Juma'a a gobe

- Masu layin za su hau yanar gizo a kyauta

- Sai dai akwai wasu sharuda kafin a dace

Labari ya zo mana cewa masu layin Glo za su gwangwaje kyauta gobe a Najeriya muddin sun sa katin waya.

Albishirin ku: Gobe masu layin GLO za su ci banza
Za a hau yanar gizo kyauta a layin GLO

Kamfanin sadarwa na Globacom na kasar za su bada goron Juma'a a gobe wanda shi ne karo na farko a Kasar domin a hau shafin gizo kyauta ba tare da ko sisi ba. Za dai a bada kyautar mega byte 200 domin a yi abin da aka ga dama.

KU KARANTA: An ceto wanda aka daure na shekara daya

Kenan dai masu layin za su hau yanar gizo a kyauta goben. Sai dai akwai wasu sharuda kafin a dace da wannan wanda shine mutum ya zama yayi amfani da katin waya na N250 ko kuma ya kashe mega byte na hawa yanar gizo 100 da kuma N150 a cikin makon jiya zuwa yau.

Kwanaki dai Hukumar NCC da ke kula da harkokin sadarwa na zamani tayi kira ga jama'a da su saurari sabon farashin hawa shafin Internet a wayoyin salula na zamani nan ba da dadewa ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An saye wani dan wasa da dan-karen tsada

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng