Labari Da Dumi-Dumi: Bola Tinubu Ya Shigo Najeriya Bayan Shafe Makonni 2 a Faransa
- Bola Ahmed Tinubu ya shigo Najeriya kwanaki bayan wata tafiya ta musamman da ya yi zuwa Turai
- Shugaban Najeriyan ya shafe makonni biyu a kasar Faransa, ba a san ainihin abin da ya fitar da shi waje ba
- Ba wannan ne karon farko da Bola Tinubu ya leka kasar ketaren ba, ya saba kai ziyara zuwa Faransa
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya dawo Najeriya cikin daren ranar Talata, 6 ga watan Fubrairu 2023.
Jirgin da a dauka shugaban Najeriyan ya shugaban Najeriyan ya sauka ne a Abuja kamar yadda NTA ta rahoto.
Masu tarbar shugaba Tinubu
Jirgin fadar shugaban kasar ya sauka a tashar Nnamdi Azikiwe da ke babban birnin tarayya kusan 9:30 na dare.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bisa al’ada, wadanda suka tarbi shugaban kasar sun hada da Ministan harkokin birnin tarayya, Nyesom Wike.
Daily Trust ta ce shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya na cikin ‘yan tarbar.
Femi Gbajabiamila yana cikin wadanda suka fi kusanci da shugaban kasar.
Tinubu ya hadu da NSA, SGF
Sauran wadanda suka yi wa Bola Tinubu maraba da dawo su ne Sanata George Akume da Malam Nuhu Ribadu.
George Akume shi ne sakataren gwamnatin tarayya, Nuhu Ribadu shi ne yake bada shawara a bangaren tsaro.
Wasu gwamnonin jihohi sun samu damar tarbo shugaban Najeriyan wanda ya shafe makonni biyu a Faransa.
Daga tashar jirgin sai shugaban kasar ya wuce masaukinsa a fadar Aso Villa.
Tun da Ajuri Ngelale ya fitar da sanarwar tafiyar, har yanzu babu wanda ya san makasudin zuwa ketaren.
Yadda Tinubu zai iske Najeriya
Shugaba Tinubu ya iso ne a lokacin da ake fama da tsadar rayuwa, lamarin da ya jawo zanga-zanga a wurare.
Jam'iyyar APC tana zargin 'yan adawa suna da hannu a zanga-zangar da aka shirya a shiyyoyin Kano da Neja.
Kira ga Shugaba Bola Tinubu
An samu rahoto cewa Gbenga Olawepo-Hashim ya fadawa Bola Tinubu a aiwatar da tsare-tsaren jam’iyyarsu ta APC.
Jam’iyyar APC tana goyon bayan a kafa ‘yan sanda a jihohi, Olawepo-Hashim ya na ganin hakan zai kawo zaman lafiya.
Asali: Legit.ng