Zanga-Zanga: Gbajabiamila da Ribadu Sun Shiga Ganawar Gaggawa da Wasu Ministoci, Bayanai Sun Fito

Zanga-Zanga: Gbajabiamila da Ribadu Sun Shiga Ganawar Gaggawa da Wasu Ministoci, Bayanai Sun Fito

  • Yayin da zanga-zanga ta barke a biranen Minna da Kano, Gwamnatin Tarayya ta shiga ganawar gaggawa kan matsalar
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa shugaban ma'aikata, Femi Gbajabiamila ya shiga ganawar da wasu Ministoci
  • Har ila yau, a cikin ganawar akwai Mallam Nuhu Ribadu wanda shi ne mai ba da shawara a kan harkokin tsaro

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Awanni bayan barkewar zanga-zanga a wasu biranen kasar, an dauko hanyar dakile matsalar.

Shugaban ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Femi Gbajabiamila da mai ba da shawara a harkar tsaro, Nuhu Ribadu sun shiga ganawar gaggawa.

An shiga ganawar gaggawa kan zanga-zanga a Najeriya
Gbajabiamila da Ribadu Sun Shiga Ganawar Gaggawa da Wasu Ministoci. Hoto: Nuhu Ribadu, Bola Tinubu, Femi Gbajabiamila.
Asali: Twitter

Mene dalilin ganawar gaggawar?

Sauran wadanda ke cikin ganawar da ake yi yanzu haka a fadar shugaban kasar akwai wasu Ministocin Tinubu.

Kara karanta wannan

Uwar gidan Shugaba Tinubu ta yi ƙus-ƙus da matan gwamnoni a Aso Villa, bayanai sun fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An fara gudanar da ganawar ce da misalin karfe 5:30 na yammacin yau Talata 6 ga watan Faburairu, cewar Channels TV.

Daga cikin Ministocin da suke cikin ganawar akwai Ministan ilimi, Dakta Tahir Mamman da na kudade, Wale Edun.

Sauran sun hada da Ministan harkokin noma, Abubakar Kyari da kuma karamin Minista a ma’aikatar, Mustapha Shehuri.

Zanga-zanga a Minna da Kano kan halin kunci

Wannan ganawar na zuwa ne bayan mata da matasa sun fito zanga-zanga a biranen Minna da Kano kan tsadar rayuwa da ake ciki.

Ganawar har ila yau, za a tattuna yadda kayan masarufi suke tashi musamman bangaren abinci, cewar Punch.

Idan ba manta ba, a jiya Litinin ce 5 ga watan Faburairu zanga-zanga ta barke a birnin Minna da ke jihar Neja kan tsadar rayuwa, cewar The Citizen.

Kara karanta wannan

An shiga rububi, Gwamnatin Tinubu ta magantu kan yadda za ta daga darajar Naira a kan dala

Ana cikin haka ne kuma wata zanga-zangar ta sake barkewa a birnin Kano da ke Arewacin Najeriya kan halin kunci da ake ciki.

APC ta zargi PDP kan zanga-zanga

Sai dai jam'iyyar APC mai mulkin kasa ta dora alhakin wannan zanga-zanga kan jam'iyyun adawa da cewa suna daukar nauyinsu.

Jam'iyyar ta ce hakan bai rasa nasaba da neman batawa gwamnatin Shugaban Tinubu suna a kasar yayin da ya ke kokarin shawo kan lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.