EFCC Ta Dakile N3bn a Wurin Kanin Ministan Buhari Daga Cikin N8bn da Ake Nema, Bayanai Sun Fito
- Hukumar EFCC ta bankado wata badakalar naira biliyan takwas da ake zargin kanin Ministan Buhari, Hadi Sirika
- Ana zargin Sirika ya bai wa kaninsa manyan kwangiloli guda hudu da suka kai naira biliyan takwas lokacin ya na Minista
- Hukumar ta dakile biliyan uku daga kanin Ministan mai suna Abubakar Ahmed Sirika a yayin bincike da ta ke yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Hukumar EFCC ta kulle asusun bankin dan uwan Ministan Buhari, Hadi Sirika dauke da biliyan uku a ciki.
Ana zargin dan uwan nashi, Abubakar Ahmed Sirika kan badakalar naira biliyan takwas a wata kwangilar ma’aikatar jiragen sama.
Mene EFCC ake zargin kanin Hadi Sirika?
Abubakar dan uwan tsohon Ministan jiragen sama da ake zargin ya bai wa kanin nashi kwangilar makudan kudade.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An cafke Abubakar a ranar Lahadi 4 ga watan Faburairu kan zargin badakalar kwangilar yayin da Sirika ke kan kujerar Minista.
EFCC na humarsu da zargin hada baki da karkatar da biliyoyin kudade da cin amana da kuma kara kudin kwangila, cewar Tori News.
Nawa hukumar EFCC ke nema a hannunsu?
Daga cikin kudaden, an gano naira biliyan uku a wani kamfani da Abubakar ke mallaka wanda mataimakin darakta ne a ma’aikatar Albarkatun Ruwa.
The Nation ta tattaro cewa an bai wa Abubakar manyan kwangiloli guda hudu a kamfaninsa na Engirios Nigeria Limited lokacin da Sirika ke Minista.
Masu bincike a EFCC sun tabbatar da cewa Abubakar shi ne babban daraktan kamfanin da ake binciken.
An kama Fasto kan badakalar N1.3bn
Kun ji cewa, hukumar yaki da cin hanci a Najeriya, EFCC ta cafke wani fitaccen Fasto, Apostle Theophilus Oloche Ebonyi kan badakalar naira biliyan 1.3.
Hukumar EFCC ta kama Ebonyi ne bisa laifin damfarar mabiyansa da wasu 'yan Najeriya ta hanyar amfani da tallafin jabu daga gidauniyar Ford har naira biliyan 1.3.
Hukumar a kwanakin nan ta yi nasarar cafke mutane da dama kan badakalar makudan kudade kuma ta na ci gaba kwacewa kudaden a hannunsu.
Asali: Legit.ng