Tsohon Hadimin Buhari Ya Caccaki Abba Gida Gida Kan Shirinsa Na Ganawa da Tinubu

Tsohon Hadimin Buhari Ya Caccaki Abba Gida Gida Kan Shirinsa Na Ganawa da Tinubu

  • Hadimin tsohon shugaban kasa Buhari, Bashir Ahmad, ya caccaki Gwamna Abba Yusuf na Kano kan shirinsa na ganawa da Shugaba Bola Tinubu saboda tsadar rayuwa a jihar
  • Gwamna Yusuf ya bayyana shirinsa na ganawa da shugaban kasar kan yiwuwar shiga tsakanin, musamman saboda 'yan kasuwa a jihar
  • Sai dai Ahmad ya ce yayin da Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas ke kulla yarjejeniya ga jiharsa a China, Gwamna Yusuf na gudun zuwa Abuja don neman a shiga tsakani

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Kano, jihar Kano - Bashir Ahmad, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya caccaki Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano kan shirin ganawa da Shugaba Bola Tinubu saboda wahalar da ake ciki a kasar.

Kara karanta wannan

Ramadan: Abba ya zauna da ‘yan kasuwan Kano, ya roki a fito da abinci da aka boye

Gwamnan ya bayyana a cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na X cewa zai gana da Shugaban kasa Tinubu saboda tsadar rayuwa a kasar.

Bashir Ahmad ya caccaki Abba Yusuf kan ganawa Tinubu
Tsohon Hadimin Buhari Ya Caccaki Abba Gida Gida Kan Shirinsa Na Ganawa da Tinubu Hoto: Bashir Ahmad, Bola Ahmed Tinubu, Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Abba Gida Gida zai gana da Tinubu

Gwamna Yusuf ya yi martanin ne yayin da ya gana da 'yan kasuwa a Kano a ranar Litinin, 5 ga watan Fabrairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya rubuta:

"Na kuma yi alkawarin ganawa da Shugaban kasa Bola Tinubu don sanar da shi halin da ake ciki, domin ya shiga tsakani."

Ga wallafan nasa:

Bashir ya bukaci Abba ya ba kananan hukumomi damar cin gashin kansu

Sai dai kuma a martaninsa ga rubutun gwamnan, Ahmad ya bayyana furucin gwamnan a matsayin mara ma'ana.

Ya ce babban yunkuri guda da gwamnan ya kamata ya yi shine bai wa kananan hukumomi 44 dake jihar damar cin gashin kansu don samun canji mai kyau.

Kara karanta wannan

Neman tabarraki: Shugaban hukumar fina-finai ta Najeriya, Ali Nuhu ya ziyarci Sarkin Kano

Ya rubuta:

"Matakin da Gwamna Abba ke shirin dauka bai da ma'ana, kuma hakan zai iya sa ayi tunanin cewa tushen wadannan matsalolin ya ta’allaka ne kawai a matakin tarayya.
"Alhalin a matsayinsa na gwamna yana rike da gagarumin iko wajen kawo sauyi a jiharmu.
"Tushe mai kyau shine bai wa kananan hukumomin mu 44 cikakken 'yancin cin gashin kansu, wanda zai iya haifar da sauye-sauye masu kyau da kuma ci gaba mai yawa a fadin jihar."

Ga rubutun a kasa:

Ka yi koyi ga Sanwo-Olu, Bashir ga Abba

A wani rubutun kuma, tsohon hadimin shugaban kasar ya yi kira ga gwamnan da ya yi koyi da takwaransa na jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, wanda yake kasar China a yanzu haka don kulla yarjejeniya.

Ya ce:

"Gwamna Sanwo-Olu ya kasance a China tsawon kwanaki yana tattauanawa da kulla yarjejeniya masu girma ga Legas yayin da gwamnanmu na Kano yake maganar zuwa Abuja neman a shiga tsakani."

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano zai je ya samu Tinubu su yi kus-kus kan wata gagarumar matsala 1 tak

Ga rubutun a nan:

Yan Kano sun koka da tsadar kwai

A wani labarin kuma, mun ji cewa farashin kwai ya yi tashin gauron zabi a jihar Kano yayin da ake shirin shiga lokacin azumin Ramadan.

Jama'a sun koka yayin da farashin kwai daya ya kai N130 sannan kiret ya kai N3100.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng