Daga Karshe Gwamnan CBN Ya Bayyana Dalilin Mayar da Wasu Ofisoshin CBN Daga Abuja Zuwa Legas

Daga Karshe Gwamnan CBN Ya Bayyana Dalilin Mayar da Wasu Ofisoshin CBN Daga Abuja Zuwa Legas

  • Olayemi Cardoso wanda ke jagorantar babban bankin Najeriya (CBN) ya faɗi dalilin mayar da wasu ofisoshin CBN daga Abuja zuwa Legas
  • Gwamnan na CBN ya bayyana an yi wa hedikwatar bankin da ke Abuja yawa shiyasa suka rage jama'a
  • Ya yi nuni da cewa cunkoson jama'an da ke hedikwatar na buƙatar a rage ta domin kada hakan ya kawo cikas ga ayyukan bankin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Olayemi Cardoso ya bayyana cewa an dauki matakin mayar da wasu ofisoshi da ma’aikata a hedikwatar bankin da ke Abuja zuwa wasu rassa ne saboda “cunkoson jama’a”.

Cardoso ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wata hira a gidan talabijin na Arise tv.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya bayyana hanya 1 da za a bi domin magance cin hanci da rashawa Najeriya

Cardoso ya fadi dalilin kwashe ofisoshin CBN
Cardoso ya ce akwai cunkoso a hedikwatar CBN da ke Abuja Hoto: @cenbank
Asali: Facebook

Da aka tambaye shi ko hedikwatar CBN na da cunkoson jama’a, sai ya ce cunkoson jama'an ya yi yawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ƙara da cewa bankin na sa ran cewa matakin zai magance matsalar cunkoson jama'an a hedikwatar bankin da ke Abuja.

"Akwai cunkoso a CBN" - Cardoso

A kalamansa:

"Gaskiyar magana, duk wanda ya zo bankin kuma ya yi hulɗa zai ga cewa akwai cunkoson jama'a. Dole ne mu ga cewa za mu iya magance matsalolin da za su iya faɗowa daga wajen da yake da cunkoson jama'a."

Ya ci gaba da bayyana cewa, CBN a matsayinsa na cibiya ta ƙasa, yana da reshe a kowace jiha ta ƙasar nan.

Sai dai gwamnan babban bankin ya ce idan aka samu yanayin da ma'aikatan da ke da ƙwarewar fasaha ke zaune a wani ɓangare kawai, hakan na iya kawo cikas ga ayyukan bankin.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya fadi babban dalili 1 da ya sa ya dakatar da fitaccen basarake a jiharsa

A cewarsa:

"Don haka wannan ya kasance ƙoƙari ne na tabbatar da cewa an mayar da ma'aikata masu ƙwarewa daga inda akwai yawansu, zuwa inda ake da ƙarancinsu."

CBN Ya Magantu Kan Faɗuwar Darajar Naira

A wani labarin kuma, kun ji cewa CBN ya bankaɗo wasu maƙudan kudade da suka kai $2.4bn waɗanda suke jawo faduwar darajar Naira.

Gwamnan CBN, Yemi Cardoso, wanda ya bayyana hakan, ya ce an gano hakan ne bayan wani bincike da aka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng