Babban Bankin Najeriya CBN Ya Gano Wani Dalili 1 Tak da Ke Jawo Faduwar Darajar Naira

Babban Bankin Najeriya CBN Ya Gano Wani Dalili 1 Tak da Ke Jawo Faduwar Darajar Naira

  • Babban bankin Najeriya ya ce ya gano dala biliyan 2.4 da suka taimaka wajen faduwar darajar Naira a kasuwar hada hada
  • Gwamnan bankin, Yemi Cardoso ya bayyana hakan a ranar Litinin, inda ya ce an samu wadanda suka yi ikirarin kudin na bashi ne
  • Sai dai binciken da bankin ya yi a cewar Cardoso, ya gano cewa ikirarin ba gaskiya bane, kuma kudin ne ke hana Naira ta samu daraja

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Babban bankin Najeriya (CBN) ya bankado wasu makudan kudade da suka kai dala biliyan 2.4 wadanda suke jawo faduwar darajar Naira da tabarbarewar kasuwar hada-hadar kudi.

Gwamnan babban bankin kasar, Yemi Cardoso, wanda ya bayyana hakan a ranar Litinin, ya ce an gano hakan ne bayan wani bincike da aka yi.

Kara karanta wannan

Gwamna Fintiri ya sha alwashin hukunta Binani da wasu kan dalili 1 tak, ya yi alkawari

Dalilin faduwar naira
Shugaban babban bankin Najeriya, Yemi Cardoso, ya bankado dalilin faduwar Naira. Hoto: Yemi Cardoso
Asali: Twitter

Bayan shafe shekaru bakwai ana boyewa jama’a bayani kan asusun CBN, masu bincike sun gano bashin dala biliyan 7 da masu zuba jari ke hankoron suna nema, rahoton Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Boyayyun kudin da ke karya darajar Naira

Hakan dai ya haifar da cikas a kasuwar hada hadar, wanda idan ba a biya ba, zai iya karya karya darajar Naira, wanda kuma hakan ke sa farashin dala ya yi ta hauhawa a kasar.

CBN ya dauki hayar Deloitte domin ya binciki ikirarin da ake yi na boyayyun kudin, Mista Cardoso ya bayyana hakan yayin wata hira da gidan talabijin na Arise.

Cardoso ya ce:

"Mun gano cewa daga cikin dala biliyan 7, kusan dala biliyan 2.4 na da matsala, waɗanda muka yi imanin cewa ba bu wani dalili da zai saka a gansu a wajen."

Kara karanta wannan

Kogi: Yan bindiga sun sace fasinjojin wasu manyan motoci guda biyu a hanyar zuwa Abuja

Rahoton na Deloitte ya gano cewa kusan dala biliyan 2.4 na kudaden da ake magana akansu na boge ne, inda masu ikirarin kudinsu ne sun gaza gabatar da shaidar hakan.

An bankado badakalar naira biliyan 12 a Kotun Koli

A wani labarin kuma, ofishin Odita-Janar na Tarayya (OAuGF) ya ce ya gano wasu makudan kudade da suka kai naira biliyan 12 da aka kashe su a Kotun Koli ba bisa ka'ida ba.

Rahoton binciken ofishin ya kuma gano yadda wasu shugabannin kotun suka karkatar da wasu kadarorin kotun don amfanin kansu, wasu kuma an cefanar da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.