Yaudara Ake Amma Aure Ba Nasara Ba Ne a Rayuwa, Jarumar Fina-Finai Ta Ce a Bar Marasa Aure Su Sarara
- Mary Njoku ta soki masu daukar aure a kayi cewa wani mataki ne na ci gaba a rayuwar dan Adam a yanzu
- Jarumar fina-finan Nollywood ta ce ya kamata a bar marasa aure su sarara kan yadda ake damunsu da aure
- Ta ce kwata-kwata ba ta dauki yin aure wani matakin nasara ba ne a rayuwa inda ta shawarci mutane a kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Legas – Jarumar fina-finan Nollywood, Mary Remmy Njoku ta bayyana matsayarta kan yin aure a rayuwar dan Adam.
Njoku ta ce kwata-kwata ba ta dauki yin aure a matsayin wani matakin nasara a rayuwa ba.
Mene Njoku ke cewa kan aure?
Ta bayyan haka ne a shafin Instagram inda ta ce bai kamata mutum ya dauka cewa yin aure nasara ba ce.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mary ta caccaki wadanda ke ganin aure a matsayin nasara a rayuwa da har suke takura wasu don su yi aure.
Ta ce tabbas aure kwata-kwata baya daga cikin matakan nasara amma samun abokin zama da ya dace shi ne komai.
Ta kara da cewa dole a bari mutane su zabi abokin zama lokacin da ya dace amma ba takura musu cewa sai sun yi aure ba.
Shawarar da Njoku ta bayar kan aure
Ta ce:
“Ya ku mata ma’aurata, abin da kuke yi ya isa haka, aure ba ya daga cikin matakan nasara a rayuwa.
“Samun abokin zama da ya dace shi ne abin da ya fi, ku ba su lokaci su yanke shawara da daukar matakin da ya dace a rayuwarsu.
“Haba! Ku bari mutane su nemo zabin ransu cikin salama ba tare da takurawa ba da wasu ke yi.”
Njoku ta ce fiye da kaso 60 na ma’aurata suna ikirarin jin dadi a aure, shi ya sa suka tunzura Ifeoma kullum ta na asibiti.
Ta shawarci mutane da su mai da hankali kan tattalin arziki inda ta roke su da subar marasa aure su sarara, cewar The Nation.
Saduwa kafin aure na taimakawa, Jarumar fim
Kun ji cewa jarumar fina-finan Nollywood, Tosin Adekansola ta bayyana amfanin saduwa kafin aure ga masu son zaman aure har abada.
Ta ce rashin saduwa kafin aure ya na lalata zamantakewa da kuma kawo cikas yayin zaman auren.
Asali: Legit.ng