Tattalin Arziki: Atiku Ya Kuma Caccakar Gwamnatin Tinubu, Ya Ce ’Yan Najeriya Sun Fidda Tsammani
- Dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 karkashin jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya caccaki gwamnatin shugaba Tinubu
- Atiku Abubakar ya yi ikirarin cewa shugaba Tinubu ya jawo tattalin arzikin kasar ya lalace kuma ya gaza gyarawa
- Ya nemi bukaci Tinubu da ya nemi taimako, yana mai buga misali da ficewar manyan kamfanoni daga kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya kalubalanci yadda shugaba Bola Tinubu ke rikon sakainar kashi akan tattalin arzikin kasar.
Atiku wanda shi ne dan takarar shugaban kasa karkashin PDP a zaben 2023 ya yi nuni da cewa 'yan Najeriya sun cire tsammani daga gwamnatin Tinubu.
Ya kuma ce tsare-tsaren gwamnati mai ci sun durkusar da kananun 'yan kasuwa, tare da tilasta manyan kamfanoni ficewa daga kasar, Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamfanoni na ficewa daga Najeriya - Atiku
A cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, ya kara da cewa ta'azzarar tattalin arziki ya nuna cewa Shugaba Tinubu ba zai iya tafiyar da Najeriya ba.
Ya ce:
"Babu wani dan Najeriya da ke a gida ko waje wanda ba ya kuka da tsarin gwamnatin nan ta fuskar tattalin arziki.
"Mun ga yadda manyan kamfanoni na duniya ke dakatar da aiki a Najeriya, suna barin kasar saboda ba mu da tsarin tattalin arziki mai kyau."
Tinubu na bukatar taimako - Atiku
Ya kuma kalubalanci kasafin 2024 da Tinubu ya sakawa hannu yana mai cewa babu hikima ko tunani mai kyau a cikin sa.
Atiku ya kara da cewa shugaban kasar ya nuna tsantsar rashin kwarewarsa a warware matsalolin da suka shafi canjin kudi na kasa-da-kasa.
Da wannan ya bukaci Tinubu da ya nemi taimako akan hanyoyin da ya kamata ya farfado da tattalin arzikin kasar da ya yi doguwar suma.
Ma'aikatan tarayya sun yi fushi da gwamnati
A wani labarin daga makon jiya, ma'aikatan tarayya sun nuna bacin ransu kan yadda gwamnati ta gaza cika alkawarinta na yi masu albashi tun a ranar Alhamis.
Rahotanni sun bayyana cewa har zuwa ranar Juma'a ma'aikatan basu ga albashin su ba, lamarin da ya ja wasu suka fara 'yan guna-guni.
Asali: Legit.ng