An Fadi Dalilin da Ya Sa Gwamnatin Tinubu Ta Fi Ta Buhari

An Fadi Dalilin da Ya Sa Gwamnatin Tinubu Ta Fi Ta Buhari

  • An bayyana cewa ƙokarin da Shugaba Bola Tinubu yayi wajen yaƙi da rashin tsaro ya fi na magabacinsa, Muhammadu Buhari
  • A nasa nazarin, Shehu Sani, wanda tsohon sanata ne, ya yi iƙirarin cewa gwamnatin Buhari ta tafiyar da CBN tamkar a ƙarƙashin gwamnatin Idi Amin
  • Tsohon Sanatan ya bayyana cewa abin da sojoji da ƴan sanda da sauran jami’an tsaro suke yi a ƙarƙashin Tinubu ya fi abin da ke faruwa a ƙarƙashin Buhari

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Sanata Shehu Sani ya yi magana kan bambancin gwamnatin Shugaba Tinubu da ta magabacinsa Muhammadu Buhari.

Tsohon sanatan na Kaduna ta tsakiya ya yi nuni da cewa gwamnatin Tinubu ta fi ta Buhari.

Kara karanta wannan

Mutane sun fusata yayin da ake zargin wani mutumi ya yi ɓatanci ga Annabi SAW a jihar Arewa

Shehu Sani ya yabi Tinubu
Shehu Sani ya yi nuni da cewa Tinubu ya fi Buhari kokari wajen magance rashin tsaro Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Shehu Sani, Muhammadu Buhari
Asali: Twitter

Sani, wanda ya yi magana a shafin X na Legit.ng a ranar Laraba, 31 ga watan Janairu, ya bayyana cewa kafin yanke hukunci kan gwamnatin Tinubu, ya kamata ƴan Najeriya su duba halin da ake ciki a baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Buhari ya lalata tattalin arziƙin Najeriya, Shehu Sani

Da yake magana kan magance matsalar rashin tsaro da cin hanci da rashawa da ya addabi ƙasar nan, tsohon sanatan ya ci gaba da cewa ayyukan jami'an tsaro a gwamnatin Tinubu ya fi abin da ya faru a gwamnatin Buhari.

A kalamansa:

“A lokacin da Buhari ya bar mulki, mutane miliyan 133 ne ke fama da talauci, muna da sama da dubu 100 da ƴan ta’adda suka kashe, an sace rabin adadin, kuma ya bar bashin sama da Naira Tiriliyan 77.

Dalilin da ya sa Tinubu ya fi Buhari

Kara karanta wannan

Tsohon hadimin Buhari ya yaba kan bambanci 1 da Tinubu ya nuna tsakanin Peter Obi da Atiku

Tsohon sanatan ya ce gwamnati mai ci ta na ƙoƙari wajen yaƙi da rashin tsaro idan aka kwatanta da gwamnatin Buhari.

A kalamansa:

"Ta fuskar tsaro ana kashe mutane, ana ci gaba da yin garkuwa da mutane, kuma ƴan ta’adda na ƙara ta’azzara, amma zan iya gaya muku, kwatankwacin abin da sojoji da ƴan sanda da sauran jami’an tsaro suke yi a yau ya fi wanda suke yi a baya. Daga Kaduna na fito, kusan ba zai yiwu mutane su tashi daga Kaduna zuwa Abuja ba, amma yanzu kaɗan-kaɗan ake samun hakan.

Shehu Sani Ya Magantu Kan Kisan Sarakuna

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya yi Allah wadai da kisan da aka yi wa wasu sarakunan gargajiya biyu a jihar Ekiti.

Shehu Sani ya bayyana cewa dole ne a nemo miyagun da suka aikata wannan ɗanyen aikin domin su fuskanci hukunci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel