Tsohon Sanatan APC Ya Fallasa Alkalai, Ya Zargi Babban Kotu da Zama Tamkar POS

Tsohon Sanatan APC Ya Fallasa Alkalai, Ya Zargi Babban Kotu da Zama Tamkar POS

  • Kotun daukaka kara ta tsige Elisha Abbo daga majalisa, har yanzu yana jin haushin hukuncin
  • Tsohon Sanatan ya ce alkalan kotun daukaka kara suna saida shari’a ne ga wanda ya fi bada kudi
  • Elisha Abbo ya yi magana a ranar Laraba a wani taron ‘yan jarida da ya kira a babban birnin Abuja

Abuja - Elisha Abbo ya wakilci mutanen Adamawa ta Arewa a majalisar dattawa ya dura kan kotun daukaka kara a Najeriya

Premium Times ta rahoto Sanata Elisha Abbo ya na sukar Monica Dongban-Mensen wanda ita ce shugabar babban kotun.

Tsohon Sanatan APC Kotu
Kotu ta kori Sanata Elisha Abbo Hoto: Reverend Amos Yohanna/Senator Ishaku Abbo
Asali: Facebook

Sanata ya soki hukuncin tsige shi a kotu

‘Dan siyasar yana zargin cewa alkalai suna fyaden shari’a, ana ba su cin hancin kudi a maimakon su yi shari’a ta gaskiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Fetur zai iya kara tsada maimakon a samu sauki da matatun gida za su fara aiki

Abbo wanda ya rasa kujerarsa a kotun bai huce ba, yana zargin an tafka kuskure a wajen ba Amos Yohanna da PDP gaskiya.

A wani taro da ya kira na ‘yan jarida a ranar Laraba, Abbo ya soki yadda aka soke zaben da aka shirya a rumfuna 253 a mazabarsa.

Abbo ya tabo Dongban-Mensen da kotunta

An rahoto shi yana jifan Dongban-Mensen da cewa ta maida kotunta kasuwar samun kudi, inda ta ke saida gaskiya a kan farashi.

Tsohon sanatan wanda yana cikin wadanda suka tantance Dongban-Mensen a majalisa, ya ce bai nemi cin hanci wajen ta a lokaicn ba.

A jawabinsa, Sanata Abbo ya yi mamakin yadda kotun daukaka kara ta zama mai kudi shi yake samun yadda yake so a shari’o’insu.

"Ya kamata duniya ta dauka cewa a lokacinki (Dongban-Mensen)ta zama abin dariya."
“Ba a taba yin lokacin da a shari’a kotun daukaka kara ta zama iya kudinka iya shagalinka, wata POS kamar yanzu ba."

Kara karanta wannan

Mai ba Jonathan shawara ya nunawa Tinubu hanyar farfado darajar Naira kan Dala

- Elisha Abbo

Sanata ya jefi yaran alkalai da zargi

Da zarar shari’a ta je babban kotun, Abbo ya ce kudinka ne zai fitar da kai, wanda yana ganin hakan ya ci karo da manufar Bola Tinubu.

Sanatan na APC ya ce ‘ya ‘yan manyan alkalai su ke bin masu kara da wadanda ake tuhuma su na neman na goro da za a bada a kotu.

Kotu ta sa Abbo ya bar Sanata

An ji kotun daukaka kara ta soke kuri’un da APC ta samu a zaben Sanatan Adamawa, ta ce Amos Yohanna ya fi yawan halatattun kuri’u.

Maimakon alkalai su ce a sake jefa kuri’u, ‘dan siyasar ya fusata ba ayi hakan ba domin a cewarsa an san shi zai yi nasara idan aka kara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng