Ta tabbata: Dangbam - Mensem ta zama shugabar kotun daukaka kara (PCA)

Ta tabbata: Dangbam - Mensem ta zama shugabar kotun daukaka kara (PCA)

A ranar Alhamis ne majalisar dattijai ta amince tare da tabbatar da nadin Monica Dongban - Mensem a matsayin shugabar kotun daukaka kara na Najeriya.

Shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmed Lawan, ya bayyana shirin bangaren yin doka na bawa kokarin gyaran bangaren shari'a duk wata gudunmawa da ta dace.

Tabbatar da Dangban - Mensem ya biyo bayan la'akari da rahoton kwamitin majalisar dattijai a kan bangaren shari'a da kare hakkin bil adama wanda Sanata Opeyemi Bamidele (Ekiti ta tsakiya) ke jagoranta.

A ranar Talata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikewa da majalisar dattawa, sunan Jastis Monica Dongban-Mensem, a matsayin sabuwar shugaba ta kotun daukaka kara domin tantancewa da tabbatarwa.

Bisa ikon da kundin tsarin mulkin kasa ya bai wa shugaba Buhari, yana neman amincewar majalisar wajen nadin Jastis Monica, a matsayin sabuwar shugabar kotun daukaka kara ta Najeriya.

Mai magana da yawun shugaban kasa Mallam Garba Shehu, shi ne ya wallafa sanarwar hakan a kan shafinsa na Twitter a Litinin, 8 ga watan Yunin 2020.

Haka kuma shugaban kasar ya tabbatar da wannan sanarwa da kansa a sakon da aka wallafa kan shafinsa na dandalin sada zumunta da Yammacin ranar Litinin.

Ta tabbata: Dangbam - Mensem ta zama shugabar kotunan daukaka kara (PCA)
Jastis Monica Dangbam - Mensem
Asali: Twitter

Kamar yadda lamarin ya zamto al'ada, hukumar shari'ar kasa, ta shawarci shugaban kasa Buhari akan nadin Jastis Dongban-Mensem a matsayin sabuwar shugabar kotun daukaka kara a kasar.

A halin yanzu Jastis Dongban-Mensem babbar mai shari'a ce a kotun daukaka kara.

Hakazalika ita ce mai rikon kwarya ta shugabancin kotun daukaka kara ta kasar nan.

A baya Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa, akwai shirye-shiryen dakatar da Jastis Monica daga zama shugaba ta kotun daukaka kara.

DUBA WANNAN: 'Masana'anta ce' - Ahmed Lawan ya fadi sirruka a kan kungiyar Boko Haram

An bankado cewa akwai kuma yunkurin da ake yi na nada Jastis Mohammed Lawal Garba, wanda ya jagoranci shari'ar kararrakin zaben shugaban kasa na 2019 a maimakonta.

Duk da cewa ana ta cece-kuce a kan Jastis Monica a matsayinta na mabiyar addinin Kirista wadda ta fito daga yankin Arewa yayin da Garba yake Musulmi.

Jaridar The Cable dai ta gano cewa al'amarin ya ginu ne a kan banbancin siyasa, kabilanci da addini.

Hukumar shari'a ta tarayya ta bayyana Monica da Lawal a matsayin wadanda za su iya maye gurbin Zainab Bulkachuwa wacce ta yi murabus a Maris din 2020 bayan ta cika shekaru 70.

Jastis Monica ta kasance 'yar asalin jihar Filato, yayin da Jastis Garba ya kasance dan asalin jihar Sakkwato.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng