Buhari ya mika wa Majalisar Dattawa sunan Jastis Monica Dongban-Mensem a matsayin shugabar kotun daukaka kara

Buhari ya mika wa Majalisar Dattawa sunan Jastis Monica Dongban-Mensem a matsayin shugabar kotun daukaka kara

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikewa da majalisar dattawa, sunan Jastis Monica Dongban-Mensem, a matsayin sabuwar shugaba ta kotun daukaka kara domin tantancewa.

Bisa lamunin da kundin tsarin mulkin kasa ya bai wa shugaba Buhari, yana neman amincewar majalisar wajen nadin Jastis Monica, a matsayin sabuwar shugabar kotun daukaka kara ta Najeriya.

Jastis Monica Dongban-Mensem
Jastis Monica Dongban-Mensem
Asali: UGC

Mai magana da yawun shugaban kasa Mallam Garba Shehu, shi ne ya wallafa sanarwar hakan a kan shafinsa na Twitter a Litinin, 8 ga watan Yunin 2020.

Haka kuma shugaban kasar ya tabbatar da wannan sanarwa da kansa a sakon da wallafa kan shafinsa na dandalin sada zumunta da Yammacin ranar Litinin.

KARANTA KUMA: Ma'aikatan NDDC 6 sun kamu da cutar korona

Kamar yadda lamarin ya zamto al'ada, hukumar shari'ar kasa, ta shawarci shugaban kasa Buhari akan nadin Jastis Dongban-Mensem a matsayin sabuwar shugabar kotun daukaka kara a kasar.

A halin yanzu Jastis Dongban-Mensem babbar mai shari'a ce a kotun daukaka kara. Hakazalika ita ce mai rikon kwarya ta shugabancin kotun daukaka kara ta kasar nan.

A baya Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa, akwai shirye-shiryen dakatar da Jastis Monica daga zama shugaba ta kotun daukaka kara.

DUBA WANNAN: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka ana wallafawa

An tattaro cewa akwai kuma yunkurin da ake yi na nada Jastis Mohammed Lawal Garba, wanda ya jagoranci shari'ar kararrakin zaben shugaban kasa na 2019 a maimakonta.

Duk da cewa ana ta cece-kuce a kan Jastis Monica a matsayinta na mabiyar addinin Kirista wadda ta fito daga yankin Arewa yayin da Garba yake Musulmi.

Jaridar The Cable dai ta gano cewa al'amarin ya ginu ne a kan banbancin siyasa, kabilanci da addini.

Hukumar shari'a ta tarayya ta bayyana Monica da Lawal a matsayin wadanda za su iya maye gurbin Zainab Bulkachuwa wacce ta yi murabus a Maris din 2020 bayan ta cika shekaru 70.

Jastis Monica ta kasance 'yar asalin jihar Filato, yayin da Jastis Garba ya kasance dan asalin jihar Sakkwato.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel