A Kara Hakuri: Minista Ya Ce Ana Daf da Cin Moriyar Kudurorin Shugaba Tinubu a Najeriya
- Gwamnatin tarayya ta roki 'yan Najeriya da su kara hakuri da matsin tattalin arziki da tsadar rayuwar da suke fuskanta
- Ministan yada labarai na kasa, Mohammed Malagi ya yi rokon yana mai cewa bai kamata 'yan Najeriya su fara korafi tun yanzu ba
- A cewar ministan, watanni bakwai da Tinubu ya yi a mulki ba su isa ace an yanke hukunci kan makomar kasar ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Ministan yada labarai na kasa Mohammed Idris Malagi ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su kara hakuri akan sauye-sauyen gwamnatin Bola Tinubu.
Tinubu, wanda ya fara mulki a 2023, ya kawo wasu sauye-sauye da suka shafi Naira da kuma cire tallafin man fetur da ake ta cece-kuce akan shi.
Wannan yunkurin ya haifar da tashin gwauron zabi na tsadar rayuwa tare da hauhawar farashin kayayyaki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Minista ya roki 'yan Najeriya su kara ba Tinubu lokaci
Amma Malagi ya ce ya san dama hakan za ta faru, amma nan gaba kadan 'yan Najeriya za su fara amfana da waɗannan sauye-sauye.
“Ina so ku tuna cewa watanni bakwai kawai shugaba Tinubu ya yi a kan karagar mulki, kowa ya san wannan karamin lokaci ne na ganin amfanin canji."
- Mohammed Idris Malagi
Ya fadi hakan ne a ranar Alhamis a shirin 'Sunrise Daily' na Channels TV.
Ministan ya kara da cewa:
"Kudurorin shugaban kasa a fili suke, burinsa shi ne Najeriya ta samu ci gaba, kuma yana aiki ba dare ba rana don cimma hakan.
"Kowace rana, ministoci da duk wani jami'in gwamnati na aiki tukuru don cimma muradun Tinubu amma har yanzu babu sakamako. Muna fatan 'yan Najeriya za su kara hakuri."
- Mohammed Idris Malagi
Gwamnati na sane da wahalar da mutane ke sha - Malagi
Ya ce gwamnati na sane da irin wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fuskanta, ministan ya tabbatar da cewa shugaban kasar na bakin kokarinsa wajen ganin an sauya yanayin.
A cewarsa, gwamnatin shugaba Tinubu a dalilin cire tallafin man fetur ta bullo da wasu matakai na dakile tasirin da hakan zai yi kan jama'a.
Ya lissafta wasu daga cikin matakan da suka hada da kyautar kudi ga ma’aikatan gwamnatin tarayya da shirin kaddamar da motocin bas na CNG a fadin kasar nan.
Ministan FCT zai kashe N30.9 don gyara makarantu
A wani labarin kuma, ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya shirya kashe naira biliyan 30.9 don yi wa makarantu kwaskwarima a Abuja.
Rahotanni sun bayyana cewa Wike zai batar da kudin ne akan gyara makarantu akalla 62 kafin nan da lokacin da shugaba Tinubu zai cika shekara daya da hawa mulki.
Asali: Legit.ng