A Wajen Kokarin Hana Lalata a Kano, An Garkame Asusun Hisbah - Sheikh Daurawa

A Wajen Kokarin Hana Lalata a Kano, An Garkame Asusun Hisbah - Sheikh Daurawa

  • Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya shaida cewa an hana su mu’amala da kudinsu da ke banki
  • Shugaban hukumar Hisbah ya ce hakan ya biyo bayan rufe masu asusu da alkali ya sa aka yi a kotu
  • Kwanaki jami’an Hisbah suka dura wasu otel, a nan ‘yan kasuwa su ke zarge da su da yi masu asara

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - A sakamakon wani kokari da ‘yan Hisbah suke yi na yaki da alfasha a jihar Kano, hukumar ta samu kan ta a matsala.

Aminu Ibrahim Daurawa ya fadawa TRT Hausa cewa wani Alkali ya bada umarni a rufe asusun hukumar Hisbah da ke banki.

Hisbah
'Yan Hisbah da Sheikh Aminu Daurawa Hoto: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Asali: Facebook

Abin da ya faru kuwa shi ne Hisbah sun shiga otel da gidajen shakatawa kwanakin baya, sai aka zarge su da haddasa asara.

Kara karanta wannan

Duk da suka daga 'yan Arewa ministan Tinubu ya dage kan mayar da FAAN zuwa Legas, ya fadi dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu masu otel sun kai karar hukumar a gaban alkali, lauyoyinsu sun yi ikirarin an yi wa wadanda suke karewa asarar dukiya.

Saboda wannan asara ta N700, 000 da N100, 000, alkali ya bada umarni hukumar ta Hisbah ta biya kudin daga cikin asusunta.

A sakamakon wannan hukunci da alkali ya zartar, dole aka rufe akawun din Hisbah da Sheikh Aminu Daurawa yake jagoranta.

Daily Trust ta rahoto Sheikh Aminu Daurawa ya na cewa wannan hukunci da aka zartar a kotu ya kawo masu cikas a aikinsu.

Hisbah ba ta san laifinta a tukuna

Shugaban hukumar yana so a sanar da su laifin da jami’ansa suka aikata, daga nan sai su dauki hayar lauyoyin da za su kare su.

Idan hukumar addinin ta gagare wanke kan ta, daga nan za a iya yanke mata hukunci yadda aka yi da gwamnatin Kano.

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya roki Tinubu ya dakatar da karin girma ga alkaliyar da ta rusa zabensa, ya fadi dalili

Malamin ya ce sun tura wakilci zuwa Akanta Janar na Kano domin ganin yadda za a warware matsalar kudin a cikin sauki.

Hisbah tana garin barazana

Wani bidiyo da Legit ta samu daga shafin malamin ya kawo yadda shehin yake bayanin irin barazanar da suke fuskanta.

Hisbah tana kokarin yakar alfasha a garuruwa. Dabarar ita ce za a janye kudi duk lokacin da suka shigo idan ba a biya ba.

Sani Rijiyar Lemo ya yabawa Hisbah

Kwanaki ne aka rahoto cewa Sheikh Sani Rijiyar Lemo ya yi magana kan ayyukan Hukumar Hisbah ganin wasu na sukar ta.

Sani Rijiyar Lemo ya ce hukumar addu'a take bukata kan irin rage barna da ta sa a gaba

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng