Abin da Na Fadawa Obasanjo Ta Kai Saura Kiris Ya Gwabje Ni Inji Lauyan Tinubu
- Wole Olanipekun yana ganin har gobe akwai matsaloli a tattare da kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999
- Gawurtaccen lauyan yana so a fito da sababbin dokoki, ba ayi kwaskwarima da garamawul da aka saba ba
- A kan wannan kira ne Olusegun Obasanjo ya nemi ya doke Wole Olanipekun, SAN a shekaru 20 da suka wuce
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Wole Olanipekun, SAN ya bada labarin wata takaddama da aka yi tsakaninsa da Olusegun Obasanjo a sa’ilin yana mulki.
A lokacin Wole Olanipekun, SAN yana shugaban NBA, Daily Trust ta rahoto shi da lauyoyi sun taba zama da Olusegun Obasanjo.
Lauyan ya ba shugaban Najeriya na lokacin shawarar ayi wa tsarin mulki garambawul. Punch ta kawo labarin nan dazu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fitaccen lauyan yana ganin akwai matsaloli tattare da kundin tsarin mulki da dokar kasar da ake amfani da su, sai an yi gyaran gaske.
Da Wole Olanipekun, SAN ya bijiro da wannan zance a gaban tsohon shugaban Najeriya a 2003, ya ce saura kiris ya kai masa nushi.
Mai girma Olusegun Obasanjo ya yi watsi da shawarar gyara tsarin mulki, bai tsaya a nan ba, har sai da ya kusa nushin shugaban na NBA.
Lauya ya soki kundin tsarin mulki
Tsohon shugaban na NBA ya nanata cewa kundin tsarin mulkin bogi ake amfani da shi.
Wasu za su nemi jin ta ya ake aiki da tsare-tsare da dokokin karya, Olanipekun ya ce kotu na amfani da duk abin da ake da shi ne.
An gayyaci Olanipekun ya gabatar da jawabi a wajen taron yaye daliban jami’ar Olabisi Onabanjo da ke Ago-Iwoye a jihar Ogun.
Kiran Wole Olanipekun zuwa ga Bola Tinubu
Masanin shari’ar ya yi suna a Najeriya, shi ya kare Bola Tinubu a shari’ar zaben 2023.
A jawabin da ya gabatar, lauyan ya roki Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya canza fasali da tsarin kasar nan tun da ya samu dama.
Idan gwamnatin Bola Tinubu ba ta yi wannan ba, Olanipekun ya ce ‘yan Najeriya da ke kasashen waje ba su yarda su dawo gida ba.
Takarar 2027 a Najeriya
Idan aka koma siyasa, za a ji labari burin Alhaji Atiku Abubakar na sake neman takara a 2027 zai gamu da cikas tun daga PDP.
Bode George ya fadawa Atiku ya horas da kannensa daga Kudu tun da Arewa sun yi shekaru takwas a lokacin Muhammadu Buhari.
Asali: Legit.ng