Gani Adams: Kundin tsarin mulki na 1999 shaidanin tsari ne

Gani Adams: Kundin tsarin mulki na 1999 shaidanin tsari ne

- Wani sananne a yankin Yarbawa yayi Allah-wadai da tsarin mulkin Najeriya

- Ya siffanta tsarin mulkin kasar da tsarin Shaidan kuma mai bai wa miyagu mafaka

- Ya kuma bayyana cewa ba za su taba bari abinda ke faruwa a arewa ya faru a yankin Yarbawa ba

Gani Adams, Aare Ona Kakanfo na kasar Yarbawa, ya ce tsarin mulkin 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) "na shaidan ne kuma na miyagu", The Cable ta ruwaito.

Adams ya fadi haka ne a ranar Laraba lokacin da yake gabatarwa a shirin Siyasar Yau, shirin gidan Talabijin na Channels.

Aare Ona kakanfo na kasar Yarbawa ya ce ana tafiyar da kasar ne bisa tsari mara kyau.

"Babbar matsalar yanzu ita ce ana gudanar da Najeriya bisa tsari mara kyau, ana gudanar da Najeriya bisa tsarin mulki mara kyau," in ji shi.

KU KARANTA: NIMC ta bai wa MTN, Airtel, da sauran wasu kungiyoyi lasisin yin NIN

Gani Adams: Tsarin mulki na 1999 shaidan ne
Gani Adams: Tsarin mulki na 1999 shaidan ne Hoto: Vanguard News
Asali: UGC

“Kundin tsarin mulkin 1999 mugu ne, na shaidan ne. Idan ba mu gyara shi ba, ba zan iya tabbatar da zaman lafiya zai ci gaba a kasar nan ba."

Yayin da yake tsokaci kan umarnin da Rotimi Akeredolu, gwamnan jihar Ondo ya bayar, ya ce makiyayan da ke aiki ba bisa ka'ida ba su bar gandun dajin jihar ba.

Adams ya ce dole ne gwamnan a matsayinsa na babban jami’in tsaro na jihar ya “dauki bijimin da kahonsa” don kare mutanensa

"Idan gwamnan bai bayar da umarnin korar ba, shin gwamnatin tarayya za ta amince wa taron gwamnoni su yi taro da gwamnatin jihar Ondo tare da gwamnonin kudu maso yamma?" Adams ya tambaya.

Ya ce rashin tsaro a arewa maso yamma da arewa maso gabas ba za a bari ya faru a kasar Yarbawa ba, ya kara da cewa kasar Yarbawa ita ce cibiyar kasuwancin kasar.

"Ba za mu iya barin abin da ke faruwa a arewa maso gabas, arewa maso yamma, ko da a ta tsakiya ya faru a kasar Yarbawa ba," in ji shi.

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta fara rabawa mata N20,000 a jihar Kaduna

“Kar ku manta cewa kasar Yarbawa ita ce cibiyar kasuwancin wannan kasar, jijiyoyin tattalin arzikin kasar nan. Don haka, dole ne gwamnatin tarayya ta san illar barazanar tsaro a kasar Yarbawa.” Ya kara da cewa.

A wani labarin, Bayarben dan gwagwarmaya, Cif Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya ce abin da aka lalata a tsohon gidansa da masu kone-kone suka kona kalla ya haura Naira miliyan 50, The Punch ta ruwaito.

Da yake bayyana abin da ya fahimta game da harin da aka kai wa tsohon gidansa, Igboho wanda ya zanta da manema labarai ya ce masu kone-konen suna harbe-harbe kafin su shiga.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.