“Motata Na da Gado”: Matashiya Za Ta Tuko Mota Daga Landan Zuwa Legas, Komai Ya Kammalu
- Pelumi Nubi, jajirtacciyar 'yar Najeriya da ta 'dauki haramar tuki daga Landan zuwa Legas, ta nunawa duniya motarta
- Musamman aka kera motar domin wannan doguwar tafiya, kuma tana dauke da wasu abubuwan da za su sa Pelumi jin dadin tafiyarta
- A cikin wani bidiyo da ta yada, Pelumi ta ce motarta na da gado da katifa da ta siya a manhajar Amazon, kuma za ta yi tafiyar ne da tukunyar gas
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Wata matashiyar budurwa 'yar Najeriya wacce ta 'dauki haramar tuki daga Landa zuwa Legas ta baje kolin cikin motarta.
Musamman aka shirya motar saboda wannan doguwar tafiya kasancewar tana dauke da yan abubuwa don jin dadin matashiyar.
Me da me motar ta kunsa?
A cikin wani bidiyo da ta yada a TikTok, Pelumi Nubi ta bayyana cewa motar na da gadon kwanciya da zai bata damar ritsawa ta yi bacci a kan hanyarta ta tafiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Pelumi ta hasko wata yar karamar katifa irin ta kwanan dalibai, wanda ta siya a manhajar Amazon musamman saboda wannan tafiya.
Haka kuma, tana da wani dan karamin bandaki, wanda za ta yi amfani da shi wajen wanka a duk inda ya kama a hanyarta ta tafiya.
Har ila yau, akwai dan tukunyar gas a cikin motar, amma dai ta ce ba a cikin motar za ta yi girki ba, dole za ta fitar da tukunyar gas din a duk lokacin da take son girka abinci.
Kalamanta:
"Na yanke shwarar nuna maku wasu daga cikin abubuwan da motata ke dauke da shi domin saukaka mani rayuwa a wannan tafiya. Da wadannan, ba ni da wani zabi da ya wuce ji tamkar ina a gida."
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
@kyngquadri:
"Ya kamata ki kasance da abubuwa kamar su turaren barkono da sauran yan kananan abubuwa saboda tsaro."
@RRY ya yi martani:
"Meya 'karfafa wannan? Ina son sani ne kawai."
@Crystabel ta tambaya:
"Wani tanadi kika yi na tabbatar da tsaron kanki?"
@Abisola Tirenikeji:
"Ki tabbata kin watsa shirin kai tsaye tsawon tafiya. Ki bari mu lura da tafiyar har zuwa karshe."
Matashi ya bugo babur daga Landan har Legas
A wani labarin kuma, mun ji cewa wani dan Najeriya mai suna Kunle Adeyanju wanda yake tattaki daga Landan zuwa Lagas, ya isa nahiyar Afrika.
Mutumin wanda yana tafiyar ne a kan babur dinsa ya sanar da hakan a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter a ranar Litinin, 25 ga watan Afrilu.
Asali: Legit.ng