Daga Landan zuwa Lagas: 'Yan Najeriya 3 da suka yi tafiyar ban mamaki a kafa da babur

Daga Landan zuwa Lagas: 'Yan Najeriya 3 da suka yi tafiyar ban mamaki a kafa da babur

  • Wasu yan Najeriya uku sun kafa tarihi ta hanyar yin tafiye-tafiye masu ban al’ajabi
  • A yanzu haka, wani matashin dan Najeriya mai suna Kunle Adeyanju, ya sa kansa tafiya daga Landan zuwa jihar Lagas
  • A watan Fabrairun 2022 ne wata matashiya, Fehintoluwa Okegbenle, ta karade jihohi 22 a kasar cikin kwanaki bakwai a kan babur dinta

Masu iya magana kan ce tafiya mabudin ilimi ne amma kuma yin tafiya mai nisa a ababen hawa kan jefa mutum a cikin halin gajiya koma raunin zuciya musamman ma idan aka ce hanya za a bi, sai ka ga mutum ya kare da ciwon jiki.

A haka ne wasu yan mutane suka yanke ma kansu duk wani jin dadi da suke ciki sannan suka yanke shawarar karade fadin jihohin kasar har da keta tekuna a kan babur. Daya daga cikinsu ma tattaki ya yi da kafa.

Kara karanta wannan

Kofar rashawa: 'Yan Najeriya sun kadu da jin farashin fom din takarar shugaban kasa N100m a APC

Daga Landan zuwa Lagas: 'Yan Najeriya 3 da suka yi tafiyar ban mamaki a kafa da babur
Daga Landan zuwa Lagas: 'Yan Najeriya 3 da suka yi tafiyar ban mamaki a kafa da babur Hoto: @lionheart1759, @FehinLean
Asali: UGC

A wannan rahoton, Legit.ng za ta leka wasu yan Najeriya uku da suka yi tafiya mai ban mamaki da tsoro a kan baburansu, daya daga cikinsu ma a kafa ya yi tasa tafiyar.

1. Kunle Adeyanju

Wani dan Najeriya mai suna Kunle Adeyanju ya yi suna a lokacin da ya bayyana cewa zai yi tattaki daga Landan zuwa jihar Lagas a kan babur dinsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A rana ta biyu da fara tafiyar tasa, har ya shafe tsawon kilomita 700. Game da kalubalen da ya fuskanta zuwa yanzu, Kunle ya bayyana cewa akwai sanyi sosai domin anyi ta zuba ruwan sama a yayin da yake kan tafiyar.

A yanzu ya isa kasar Spain, yan Najeriya da dama da ke karanta Karin bayani kan tafiyar tasa, sun ce za su so binsa idan ya yanke shawarar komawa Landan daga Lagas.

Kara karanta wannan

Nisan kwana: Dan takarar kujerar majalisar jiha ya tsallake rijiya da baya a harin 'yan bindiga

2. Fehintoluwa Okegbenle

Matashiyar ‘yan Najeriya, Fehintoluwa Okegbenle, ta yi suna a yanar gizo lokacin da ta shirya zuwa fadin Najeriya ta hanyar amfani da babur dinta. Ta kammala wasu daga cikin tafiye-tafiyen nata cikin wasu yan awowi.

A 2022, Fehintoluwa ta saki hotuna inda ta ce ta je jihohi 22 na kasar a kan babur dinta.

3. Dahiru Buba

Sakamakon farin ciki da nasarar zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2015, wani dattijo mai suna Dahiru Buba, ya yi tattaki daga Gombe zuwa Abuja a matsayin nasa gudunmawar.

Shekaru bayan haka, mutumin ya bayyana a 2020 cewa har yanzu bashi da aikin yi kuma iyalansa na shan bakar wahala duk da tattakin da ya yi ma shugaban kasar. Ya yi korafin fama da ciwon jiki ta sanadiyar tafiyar da ya sha da kafa.

Kwanaki bayan labarinsa ya karade shafukan sadarwa, gwamnati ta kai hankali wajensa sannan ta bashi kudi naira miliyan 2 da mota domin saukaka masa.

Kara karanta wannan

Bincike: Da gaske ne Amaechi ya kai wa shugaban APC jakunkunan kudi yayin da ya ziyarcesa?

Abun mamaki: Hotunan yarinya ƴar firamare tana gyaran motoci ya jawo cece kuce a yanar Gizo

A wani labarin, wata yarinya 'yar makarantar firamare ta haifar da ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta bayan hotunanta sun bayyana inda take gyaran motoci.

Da ya wallafa labarin a shafin Twitter tare da hotunan ta a bakin aiki, @AD_Kwatu ya ce yarinyar da aka bayyana da suna Khadija ta kasance mai gyaran motoci wacce ta kware wajen gyaran birki kuma har yanzu tana zuwa makaranta duk da aikin ta.

Ya wallafa:

"Haɗu da Khadija!!" Dalibar makarantar firamare wacce ta kware wajen gyara birkin mota. Ta fito daga Paiko, jihar Neja. Ba ta yin talla, tana zuwa makaranta kuma tana da kwazo wurin aiki."

Asali: Legit.ng

Online view pixel