London zuwa Legas a babur: 'Dan Najeriya ya kai Spain, ya ci nisan 702km daga 12,000km

London zuwa Legas a babur: 'Dan Najeriya ya kai Spain, ya ci nisan 702km daga 12,000km

  • Wani 'dan Najeriya, Kunle Adeyanju, ya isa kasar Spain a tattakin da ya yi na kwanaki 25 daga Landan zuwa Legas a babur
  • Kunle ya bayyana yadda a ranarsa ta biyu yana tafiyar ya yi sa'a da yanayin gari mara dadi, sanyi ya nemi ya gigita shi
  • 'Yan Najeriya da dama sun yi martani karkashin wallafar inda suka yi ta jinjina masa, yayin da wasu suka yi ta zolayarsa da cewa zasu so suyi tafiyar tare dashi

Wani mutumi 'dan Najeriya, Kunle Adeyanju, wanda yayi tafiya mai nisan gaske inda yayi burin tafiya daga London zuwa Legas a kan babur ya bada labarin yadda tafiyarsa take kasance.

A wata wallafa da aka yi a ranar Laraba, 20 ga watan Afirilu, mutumin ya bayyana yadda ya yi tafiya mai nisan kilomita 720 a rana ta biyu da ya fara tafiyar, inda ya taso daga Bourges cikin Faransa zuwa Girona a Spain.

Kara karanta wannan

Daga Landan zuwa Lagas: 'Yan Najeriya 3 da suka yi tafiyar ban mamaki a kafa da babur

'Dan Najeriya da ya sha alwashin zuwa London daga Legas a babur ya kai Spain, ya cinye 702km daga 12,000km
'Dan Najeriya da ya sha alwashin zuwa London daga Legas a babur ya kai Spain, ya cinye 702km daga 12,000km. Hoto daga @lionheart1759
Asali: Twitter

Jajirtaccen mutumin ya bayyana yadda a ranarsa ta biyu na tafiyar tayi matukar galabaitar da shi, duba da irin bakar wahalar da ya sha saboda yanayin gari.

Kunle ya ce, ya fuskanci matanancin sanyin gari kamar kankara da iska mai karfi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Duk a irin wahalar tafiyar da ya sha, matafiyin yayi farin cikin isa wurin da yaci burin zuwa irin Millau Viaduct, ginin da ke da tsawon 336.4m (sawu1,104 ).

'Yan Najeriya sun yi martani

Ga wasu daga cikin tsokacin mutane karkashin wallafar:

@barnabasjohnnie ya ce: "Baba ya aje tarihi ga yara a lokacin da ya yi rayuwa. Idan har kwana 20 zai dauka ka gama tafiya a kan babur daga Legas zuwa Landan, to a nawa lissafin, zai iya kai ni kwana 50 a kekena."
@dammy_pk ta ce: "Babban abunda ke da mahimmaci shi ne, ina rokon ka da idan zaka koma daga Legas zuwa Landan, ka sanar min."

Kara karanta wannan

Nisan kwana: Dan takarar kujerar majalisar jiha ya tsallake rijiya da baya a harin 'yan bindiga

@_shotbytwitwi ya ce: "Baba ba ka aje wa yara taswira ba. Wacce za mu dauka mu fara namu tafiyar yanzu."
@phemmyne ta ce: "Aikin ka na kyau, ina fatan za ka isa lafiya, Ubangiji ya sa albarka."

2022: Manyan biloniyoyi mata 10 na duniya, sunayensu, kasa da adadin dukiya

A wani labari na daban, daga cikin biloniyoyi 2,668 na shekarar 2022 da Forbes ta fitar, mata kadan aka samu. An samu 327, kasa da 328 na shekarar da ta gabata (har da matan da dukiyarsu ta hada da ta mazansu, 'ya'ya ko 'yan uwa) suna da jimillar $1.56 tiriliyan fiye da ta shekarar da ta gabata da ta kai $1.53 tiriliyan.

Da yawa daga cikin hamshakan matan nan, 226 daga cikinsu sun samu dukiyarsu ne ta hanyar gado. Sun hada da mata uku na farko a duniya masu tarin arziki. Akwai L'Oreal wacce ta gaji Francoise Bettencourt Meyers, Walmart, magajiyar Alice Walton da Julia Koch, wacce ta gaji masana'antun Koch bayan mutuwar mijinta David Koch a shekarar 2019.

Kara karanta wannan

Daga cakwalkwali zuwa makaranta: Yadda Ahmed Musa ya tallafi yaro da danginsa a Legas

Asali: Legit.ng

Online view pixel