Karfin hali: Yadda aka gano wata motar da aka sato daga Kanada zuwa Najeriya

Karfin hali: Yadda aka gano wata motar da aka sato daga Kanada zuwa Najeriya

  • An gano wata motar da aka sato daga kasar Kanada aka kawo ta Najeriya domin a sayar cikin sauki
  • Rahoton da muka samo ya bayyana yadda wasu barayi suka sace motar wani, har ya cire rai amma aka gano ta a Najeriya
  • Wannan lamari dai ya ba mai motar mamaki, inda yace lallai wannan babban aiki ne abin a yaba wa jami'ai

Legas - An gano wata mota Toyota Highlander kirar shekarar 2017 da aka sace daga titin Ontario a kasar Kanada zuwa Najeriya.

An ce motar mallakin Ahmad Abdallah ta bace ne daga Ontario a watan Satumban da ya gabata, kamar yadda kafar yada labarai ta CTV ta ruwaito.

Yadda wani ya sato mota daga kasar waje
Karfin hali: Yadda aka sato mota daga Canada, aka gano ta a Najeriya | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

An tattaro cewa mai motar cire rai da gano motar bayan da aka rasa yadda za a gano inda barayin motar suka tafi da ita.

Kara karanta wannan

2023: PDP ce dai kadai za ta kai 'yan Najeriya ga tudun mun tsira, inji Saraki

Fiye da watanni shida bayan haka, sashen bincike na CTV ya ce ya sami damar gano motar - tana ajiye a wani yanki na Legas a Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan ganin bidiyon motarsa da aka mannawa allon talla, Abdallah ya fahimci yadda tsagerun da suka sace motar tasa suk a kware a iya sata, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Ya ce:

“Na samu kira daga gare ku. Kun aiko min da hoton motata. Oh hakan ya bani mamaki.”

Lamarin Abdallah wata 'yar karamar taga ce a cikin babbar matsalar satar motoci da ke addabar garuruwa a fadin kasar Kanada, musamman ma a yankin Greater Toronto.

A watan Agustan 2021, Zainab Ahmed, ministar kudi, kasafi da tsare-tsare ta kasa ta ce yawancin motocin da aka shigo da su Najeriya na sata ne, kamar yadda FIJ NG ta tattaro.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan bindiga sun kai wa motar kudi farmaki a Imo

Namijin duniya: Mutumin da ya hau babur daga Landan zuwa Legas ya shigo Afrika a rana ta 6 a tafiyarsa

A wani labarin na daban, wani dan Najeriya mai suna Kunle Adeyanju wanda yake tattaki daga Landan zuwa Lagas, ya isa nahiyar Afrika.

Mutumin wanda yana tafiyar ne a kan babur dinsa ya sanar da hakan a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter a ranar Litinin, 25 ga watan Afrilu.

Da yake sanar da isowarsa nahiyar Afrika, jarumin mazan ya wallafa wani hotonsa kusa da wata alama da ke nuna cewa lallai yana kusa da birnin Casablabca na kasar Moroko. Moroko na arewacin Afrika.

Asali: Legit.ng

Online view pixel