Namijin duniya: Mutumin da ya hau babur daga Landan zuwa Legas ya shigo Afrika a rana ta 6 a tafiyarsa

Namijin duniya: Mutumin da ya hau babur daga Landan zuwa Legas ya shigo Afrika a rana ta 6 a tafiyarsa

  • Kunle Adeyanju, hazikin dan Najeriya da ke tuko babur daga Landan zuwa Lagas ya isa nahiyar Afrika
  • Kunle ya yi hoton kansa wanda ke nuna yana kusa da Casablanca, kasar Moroko sannan ya watsa a yanar gizo
  • Jarumin mazan ya sanar da labarin tafiyar tasa a makon da ya gabata, yana mai cewa tafiyar kilomita 12,000 ne wanda zai shafe kwanaki 25 kafin a kammala

Wani dan Najeriya mai suna Kunle Adeyanju wanda yake tattaki daga Landan zuwa Lagas, ya isa nahiyar Afrika.

Mutumin wanda yana tafiyar ne a kan babur dinsa ya sanar da hakan a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter a ranar Litinin, 25 ga watan Afrilu.

Namijin duniya: Dan Najeriya da ke tuka babur daga Landan zuwa Lagas ya shiga Afrika a rana ta 6
Namijin duniya: Dan Najeriya da ke tuka babur daga Landan zuwa Lagas ya shiga Afrika a rana ta 6 Hoto: @lionheart1759
Asali: Twitter

Kunle ya isa Casablanca, kasar Moroko

Da yake sanar da isowarsa nahiyar Afrika, jarumin mazan ya wallafa wani hotonsa kusa da wata alama da ke nuna cewa lallai yana kusa da birnin Casablabca na kasar Moroko. Moroko na arewacin Afrika.

Kara karanta wannan

Kin jinin Musulmi: China ta yi Allah wadai da wadanda suka kona al-Qur'ani a Sweden

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan ce rana ta shida da fara tafiyar tasa, kasancewar ya fara ta ne a ranar 19 ga watan Afrilu, 2022.

Da wannan nisa da ya yi a tafiyar tasa, ba a sani ba ko tafiyar za ta dauke shi kasa da kwanaki 25 da ya shirya yi tun farko.

Kunle na tattakin ne domin tara kudi da zai tallafawa yaki da cutar shan inna sannan ya taimaka wajen samar da tsafta. Yana kokarin tara naira miliyan 20.

Kalli wallafarsa a kasa:

Yan Najeriya sun yi martani

@De_Oretor ya ce:

“Dan Allah yallabai ta yaya ka tsallaka daga Gibraltar zuwa Afrika ba tare da gada ba?...ina tsammanin ta jirgin ruwa.”

@MrMalvins ya yi martani:

“Allah ya tsare hanya yallabai…Yan sandan Naija, dan Allah kada ku bamu kunya idan mutumin nan ya iso Lagas…Dan Allah.”

Kara karanta wannan

London zuwa Legas a babur: 'Dan Najeriya ya kai Spain, ya ci nisan 702km daga 12,000km

@AdexAdebukola ya mayar da martani:

"Wowwwwwww....... Madalla. Da kyau yallabai. Kawai na matsa na sani ne... Ta yaya za ka koma UK? Hanya ko sama? Kuma za ka so bayyana matsalolin da ka fuskanta a haka."

London zuwa Legas a babur: 'Dan Najeriya ya kai Spain, ya ci nisan 702km daga 12,000km

A baya mun kawo cewa wani mutumi 'dan Najeriya, Kunle Adeyanju, wanda yayi tafiya mai nisan gaske inda yayi burin tafiya daga London zuwa Legas a kan babur ya bada labarin yadda tafiyarsa take kasance.

A wata wallafa da aka yi a ranar Laraba, 20 ga watan Afirilu, mutumin ya bayyana yadda ya yi tafiya mai nisan kilomita 720 a rana ta biyu da ya fara tafiyar, inda ya taso daga Bourges cikin Faransa zuwa Girona a Spain.

Jajirtaccen mutumin ya bayyana yadda a ranarsa ta biyu na tafiyar tayi matukar galabaitar da shi, duba da irin bakar wahalar da ya sha saboda yanayin gari.

Kara karanta wannan

Daga Landan zuwa Lagas: 'Yan Najeriya 3 da suka yi tafiyar ban mamaki a kafa da babur

Asali: Legit.ng

Online view pixel