An Cusa Tinubu a Lungu, ‘Yan Bindiga Sun Nemi N100m Kafin Sakin ‘Yan Makarantan Ekiti
- ‘Yan bindiga sun yi nasarar awon gaba da wasu dalibai da ma’aikatan makaranta a kauyen jihar Ekiti
- An sanar da jami’ai mummunar kaddarar da ta aukawa ‘yan makarantar Apostolic Faith Group
- Idan ana son a sake ganinsu, ‘yan bindigan sun bukaci a tanadi N100m a matsayin kudin fansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Ekiti - ‘Yan bindigan da suka yi garkuwa da ‘yan makaranta da ma’aikatan Apostolic Faith Group of Schools sun nemi kudin fansa.
Punch tace ana neman N100m a matsayin kudin fansar wadannan bayin Allah da aka dauke daga makarantar Apostolic Faith Group.
Yadda aka dauke 'yan makaranta a Ekiti
Shugabar makarantar da ke garin Ekiti, Boje Olanireti ta shaida haka da ta zanta da jaridar a yammacin ranar da abin ya faru.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Boje Olanireti ta ce an tare motar ne minti biyar bayan ta bar makarantar, a cewarta tsakanin 3:30 zuwa 4:00 aka yi aika-aikar.
Makarantar tana kauyen Emure ne, motar kuma tana kan hanyar komawa garin Eporo, yana faruwa aka sanar da jami’an tsaro.
'Yan bindiga suna neman kudin fansar N100m
Da farko ‘yan bindigan sun bukaci a biya N10m a kan kowane mutum daya lokacin da suka kira mijin wata malama da ke hannunsu.
Daga baya suka sanar da shugabar makarantar sun yi wa dukansu kudin goron N100m, lamarin ne ya sa 'dan majalisa ya fashe da kuka.
Rahoton ya ce wani wanda abin ya shafa a garin Eporo Ekiti ya tabbatar da ana neman N100m a matsayin kudin fanso mutanen tara.
An fara cafke wasu mutane
A wani kauli daga Vanguard an ji cewa miyagun ‘yan bindigan sun bukaci a tanadi N30m. Tuni an cafke wasu mutane biyar da ake zargi.
Dakarun Amotekun da wasu 'yan sa kai sun cafke wasu mutane dauke da adda da wayoyi a jeji, za a binciki ko suna da hannu a ta'adin.
Sarkin Aremo, Mai martaba Clement Akinola ya bukaci a agaza masu. Yanzu haka da lamarin ya faru shugaba Bola Tinubu yana Faransa.
An ji labari miyagun ‘yan bindiga sun yi kwantan-bauna a Emure ne suka tare motar da ta dauko dalibai bayan an kashe wasu Sarakuna.
Dalibai 25 ne a cikin motar, da suka tare su, sai suka harbi tayoyin, suka dauko yara biyar da ma’aikata hudu, daga nan aka ce sauran su tafi.
Asali: Legit.ng