Duk da 'Yarsa Na Aiki a CBN, Sanatan APC Ya Caccaki Mayar da FAAN, CBN Zuwa Legas
- Sanata Ali Ndume, ya dage cewa mayar CBN da FAAN zuwa Legas zai haifar da illa a siyasance
- Ndume ya ce saboda ƴarsa tana aiki CBN ba zai hana shi faɗin gaskiya game da shirin mayar da hukumomin zuwa Legas ba
- Sanatan mai wakiltar mazaɓar Borno ta Kudu, ya ce ya kamata Shugaba Bola Tinubu ya tuna cewa zai nemi ƙuri’un ƴan Arewa a 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ali Ndume, shugaban masu rinjaye na majalisar dattijawa, ya ce ƴarsa tana aiki a babban bankin Najeriya (CBN).
Ndume ya ce kalaman da ya yi kan yunƙurin mayar da hedikwatar hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya FAAN da wasu ofisoshin CBN zuwa Legas "gaskiya ce tsantsa".
Ya bayyana haka ne a wata hira da jaridar TheCable a ranar Litinin, 29 ga watan Janairu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kalamansa:
"Ko da ƴata tana aiki a CBN, shin ita kaɗai ce za a mayar da ita Legas? Akwai ɗaruruwan mutanen da ke shirin ƙaura zuwa Legas. A duk lokacin da irin wannan al’amari ya taso, maimakon a magance matsalar, jama’a da wasu ƴan jarida za su mayar da hankali kan mai maganar, ba maganar da yake yi ba."
Ƴan Arewa za su maida biki a 2027
Sanatan ya ƙara da cewa kalaman nasa na cewa mayar da ofisoshin na da illa a siyasance gaskiya ne, domin Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai buƙaci ƙuri’u daga Arewacin Najeriya.
"Shin ba ku ga irin martanin da dattawan Katsina suka yi ba, ƴan Arewa gaba ɗaya suna adawa da wannan matakin. Shin ba gaskiya ba ne cewa zai nemi ƙuri'un ƴan Arewa a 2027?
"Shin ba gaskiya ba ne ƴan Arewa ko ƴan adawa za su yi amfani da hakan ba? Yanzu su [ɓangaren arewa] suna ce mana 'Mun ce muku mutumin nan akwai shi da ƙabilanci, ku duba abin da yake yi. A cikin shekara ɗaya ya fara yunƙurin cutar da Arewa."
Ma'aikatan CBN Za Su Fara Aiki a Legas
A wani labarin kuma, kun ji cewa ma'aikatan babban bankin Najeriya (CBN), guda 1500 ne za su fara aiki a Legas.
Ma'aikatan dai sune waɗanda aka ɗauke ofisoshinsu daga babban birnin tarayya Abuja zuwa birnin na Legas.
Asali: Legit.ng