“Matata Ta Mayar da Hankali Kan Harkokin Addini Bata Kula da Ni”, Miji Ya Nemi a Raba Aurensu
- Wani magidanci mai suna Aku Bakari, ya yi karar matarsa Mary a gaban kotu a yankin Nyanya saboda rashin daraja aure
- Mista Bakari ya zargi matarsa da fifita coci a kansa da yaransu, ta kai har bata san ya suke ci ko suke sha ba
- Ya kuma bayyana cewa saboda sonta ga harkokin cocin, wasu lokutan tun ranar Juma'a take tafiya kuma ba za ta dawo ba ranar Lahadi da yamma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Abuja - Wani ma'aikacin gwamnati mai suna Mista Aku Bakari ya maka matarsa, Mary, gaban wata kotun gargajiya da ke yankin Nyanya a ranar Juma'a, 26 ga watan Janairu, kan zargin tsunduma a harkokin coci.
A karar da ya shigar na neman a raba aurensu, magidancin wanda ke zaune a yankin Nyanya, da ke babban birnin tarayya, ya zargi matar tasa da yin watsi da harkokinta a matsayinta na matar aure kuma uwa.
Matata na shafe kwanaki a coci, magidanci
Ya bayyana cewa sam matar bata da lokacinsa da na yaransu, illa dai kawai burinta shine zuwa coci a kodayaushe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mista Bakari ya ce wasu lokutan ta kan tafi coci tun ranar Juma'a sannan ta kwana a can har zuwa yammacin ranar Lahadi.
"Bata damu da sanin ko mun ci abinci ko bamu ci ba," cewar mijin.
Mai shigar da karar ya fada ma kotun cewa matar ta yi watsi da harkokinta kacokan a matsayin matar aure saboda coci.
An sauya tunanin matata a kotu, magidanci
Ya kuma ce ya yi kokarin hana matar tasa zuwa wannan coci amma sam ta ki bin umurninsa, rahoton Vanguard.
Bakari ya ci gaba da cewa:
"Muna zamanmu lafiya tare a matsayin mata da miji sai a 2010, lokacin da na fara ganin wasu bakin dabi'u a tattare da matata musamman a yanayin shigarta.
"Ta daina sanya dan kunne da sarkoki, tana ikirarin duk wadannan abubuwan na shaidanu ne."
"Lokacin ne na lura cewa ta daina halartan cocin da iyalinmu ke zuwa, sannan ta koma halartan wani cocin inda a nan ne ake yi mata rufa ido. Na fada mata ta daina, amma ta ki akan wannan ne nake fatan sakinta."
Sai dai kuma, wacce ake karar Mary, ta karyata zarge-zargen da ake yi mata yayin da ta bayyana a kotun.
Alkalin kotun, Doocivir Yawe, ya shawarci ma'auratan da su yi sulhu a tsakaninsu don saboda yaransu sannan ya dage shari'ar zuwa 30 ga watan Janairu, don ci gaba da zama, rahoton Daily Post.
Amarya ta yashe kawayenta ta bar gari
A wani labarin, mun ji cewa wata mai amfani da dandalin X, @AkiMarlin, ta ba da labarin yadda wata yar kasuwa, wacce ke sana'arta a kusa da jami'ar jihar Imo, Owerri, ta yaudari kawayenta kimanin su 60.
A wani labari da ya yi fice a dandalin X, @AkiMarlin ta ce yar kasuwar ta sayarwa kawayen nata su 60 ankon biki da mafici gabannin bikinta.
Asali: Legit.ng