Emefiele: EFCC Ta Shiga Bibiyar Kamfanonin Kasar Waje a Binciken Dala Biliyan 347

Emefiele: EFCC Ta Shiga Bibiyar Kamfanonin Kasar Waje a Binciken Dala Biliyan 347

  • Babban bankin CBN ya rabawa kamfanoni kudin kasar waje masu yawa a tsakanin shekarun 2014 da 2023
  • Hukumar yaki da rashawa ta EFCC tana zargin wasu kamfanonin ketare suna da hannu a badakalar kudin da aka yi
  • Godwin Emefiele wanda aka dakatar daga aiki bayan Bola Tinubu ya rike bankin kasar; CBN a lokacin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Hukumar EFCC mai yaki da rashin gasiya tana binciken yadda aka rabawa kamfanoni $347bn a Najeriya na shekaru kusan goma.

Binciken ya shafi abubuwan da suka faru daga Junairun 2014 zuwa Yunin 2023 kamar yadda Punch ta fitar da rahoto a makon nan.

EFCC.
Shugaban EFCC yana binciken aikin CBN Hoto: @officialEFCC
Asali: Twitter

Abin da hakan yake nufi shi ne hukumar ta EFCC ta fadada binciken rabon kudin kasar wajen da take yi a kamfanonin gida da ketare.

Kara karanta wannan

Dara za ta ci gida yayin da shugaban EFCC ke fuskantar dauri a gidan kaso kan dalili 1 tak

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A haka aka gano kamfanonin Najeriya da na kasar waje sun samu kusan $350bn daga hannun babban bankin na Najeriya watau CBN.

Alkaluman sna cikin rahoton yadda aka yi amfani da kudin kasashen waje a bankin CBN musamman a lokacin Godwin Emefiele yana ofis.

Tun da Ola Olukoyede ya karbi ragamar hukumar aka fara binciken ayyukan CBN.

EFCC za ta tabo kamfanonin waje

Jaridar tace kamfanonin ketare da za a bincika sun kunshi Crane Currency Limited, Gleseck+Deverint GmbH da kamfanin De La Rue Ltd.

Haka kuma ana binciken abubuwan da suka faru a Oberthur Fiduclaire SAS da Orelll Fussli.

Takardar da aka samu daga EFCC

Wata ma’aikaciyar EFCC, Hadiza Junaidu, ta aika takarda da lamba CB:4000/EFCC/DOPS/VOL.28/104 tana neman bayanan rabon daloli.

Takardar jami’ar ta nuna za a binciki kamfanonin kasashen wajen bisa zargin sabawa dokoki da ka’idojin shiga da fitar da kaya a Najeriya.

Kara karanta wannan

Zargin cin hanci: EFCC za ta binciki ‘dan siyasar da ya fi kowa dadewa a majalisa

Junaidu ta bada umarni a zagaya da takardar zuwa ga sauran jami’an hukumar.

Abin da ba a tabbatar ba shi ne lokacin da bankin CBN zai tsaida bada kudin kasashen waje ga kamfanoni da ke kasuwanci a waje.

EFCC da binciken msu mulki

Akwai tsofaffin gwamnoni daga ciki har da ministocin Bola Tinubu da aka ji suna cikin wadanda EFCC ta ke bincike kan su a halin yanzu.

A jerin akwai tsofaffin gwamnonin Ekiti, Kano, Enugu, Zamfara, Delta, Ribas da Abia.

Asali: Legit.ng

Online view pixel