Labari Mai Zafi: Jami'an EFCC Sun Dura Ofishin BUA Bayan Lalube Kamfanin Dangote

Labari Mai Zafi: Jami'an EFCC Sun Dura Ofishin BUA Bayan Lalube Kamfanin Dangote

  • Ma’aikatan hukumar EFCC sun kewaye kamfanin BUA da ke Legas kamar yadda aka yi a na Aliko Dangote
  • Ana tunanin jami’an suna binciken kudin kasashen waje ne da bankin CBN ya rabawa wasu kamfanoni
  • Zargin da ake yi shi ne BUA yana cikin kamfanonin da aka ba Dalolin, zancen da ba a iya tabbatarwa ba

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Lagos - Dakarun hukumar EFCC sun zagaye ofishin kamfanin BUA da ke Legas tun dazu.

Wani rahoto da aka samu daga Punch a yammacin Alhamis, ya ce jami’ai su na ofishin da ke Victoria Island a jihar Legas.

Kamfanin BUA
EFCC sun je Kamfanin BUA hoto: www.linkedin.com
Asali: UGC

EFCC daga Dangote sai BUA

Hakan yana zuwa ne ‘yan awanni kadan bayan an kai wani samame a ofishin kamfanin Dangote da ke garin na Legas.

Kara karanta wannan

Emefiele: Dangote ya shiga matsala bayan EFCC ta dira a babban ofishinsa, bayanai sun fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ofishin kamfanin BUA da Abdussamad Rabiu ya mallaka yana kan titin Churchgate ne a Unguwar nan ta Victoria Island.

Tun kimanin karfe 3:00 na yamma jami’an EFCC su ka fara lalube ofishin, har zuwa yanzu babu tabbacin sun bar wurin.

Meya kai EFCC ofishin BUA?

Wata majiya ta ce hukumar yaki da rashin gaskiyar tana binciken kudin kasashen waje da aka ba wasu kamfanoni 52 ne.

Daga cikin wadannan kamfanoni da ake tuhuma akwai BUA Plc da Dangote Plc wanda attajiran Kano su ka mallaka.

Kamfanonin sun samu kudin kasashen waje ne a lokacin da Godwin Emefiele yake gwamna a babban bankin CBN.

Majiya daga hukumar EFCC

"Jami’anmu su na ofishin BUA da ke Lagos Island a yanzu.
Hukumar (EFCC) su na kuma binciken kamfanin BUA PLC kamar yadda aka binciki Dangote Plc, saboda zargin son kai wajen rabon kudin ketare da tsohon gwamnan CBN, Emefiele ya yi, wanda hakan ya sabawa dokoki da ka’idojin CBN."

Kara karanta wannan

"Manyan coci za su ruguje": Jerin malamai 2 da suka hangowa kiristoci matsala a 2024

- Wani ma'aikacin EFCC

EFCC sun shiga ofisoshin BUA

Da aka tuntubi Dele Oyewale a matsayinsa na kakakin hukumar ta EFCC, ya tabbatar da wannan zance kamar yadda aka rahoto.

Amma Oyewale ya ce ba zai iya bayanin abin da ya kai ma’aikatansu kamfanonin ba.

Dangote ya sauko a 2024

Kuna da labari cewa idan aka yi lissafi da kudin Najeriya, dukiyar da Elon Musk ya mallaka ta zarce Naira tiriliyan 200 a shekarar nan.

An ji cewa Johann Rupert mai shekara 73 da haihuwa ya sha gaban Aliko Dangote idan ana maganar masu kudin nahiyar Afrika a yau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel