Kannywood: Hotunan kafin aure na Rahama Sadau da Sadiq Sani Sadiq sun tayar da kura

Kannywood: Hotunan kafin aure na Rahama Sadau da Sadiq Sani Sadiq sun tayar da kura

Fitattun jaruman finafinan Hausa wato Sadik Sani Sadik da Rahma Sadau da alamun bayyanar soyayya a tartare da su biyo bayan hotunansu dake nuna alamun akwai soyayya mai tsananin karfi a tsakaninsu.

Jarumi Sadik Sani ya baiyana cewa soyayya tana da dadi koda a ce kana da mata za ka iya karawa. Da alamu akwai yiyuwar aure a tsakanin jaruman.

Kannywood: Hotunan kafin aure na Rahama Sadau da Sadiq Sani Sadiq sun tayar da kura

Kannywood: Hotunan kafin aure na Rahama Sadau da Sadiq Sani Sadiq sun tayar da kura
Source: Facebook

KU KARANTA: An kama buhunnan dangwalallun kuri'u 7 a Jigawa

Legit.ng Hausa ta samu cewa hotunan jaruman wadanda suka soma karade dandalin sadarwar zamani tun jiya ya zuwa yanzu sun soma haifar da zazzafar muhawara tare da cece-kuce musamman ma a tsakanin masoyan jaruman.

Wasu dai na ganin hakan yayi masu daidai sannan kuma suka bayyana matukar jin dadin su idan har hakan ta tabbata yayin da kuma wasu ke ganin cewa watakila an dauki hotunan ne a yayin daukar wani shirin fim.

A wani labarin kuma, Dai dai lokacin da jarumai a masana'antar shirya fina finan Hausa ke ta kara tsunduma kan su a cikin harkokin siyasa, ana cigaba da samun sauyin sheka daga wata jam'iyya zuwa wata a tsakanin jaruman, mazan su da matan su.

A yau ma mun samu labarin cewa daya daga cikin fitattun jaruman na Kannywood mata, mai suna Fati KK ta shelanta sauya shekar ta daga tafiyar dan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar adawa ta PDP watau Alhaji Atiku Abubakar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel