Da Gaske Ake Yi: Hadimar Shugaban Kasa Ta Fadi Rukunin Ministocin da Za a Sallama a Ofis
- Hadiza Bala Usman ta sake jaddada zancen korar duk wani minista da ya gaza sauke nauyinsa
- Mai taimakawa shugaban kasar ta nanatawa wakilan gwamnati haka a wani taro da aka yi a Uyo
- Hadimar tace gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ba za tayi sakaci da alkawuran da tayi wa jama’a ba
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Mai taimakawa shugaban kasa wajen harkar manufofi da tsare-tsare, Hadiza Bala Usman ta nanata za a sallami wasu ministoci.
The Cable ta rahoto Hadiza Bala Usman tana cewa Bola Ahmed Tinubu zai yi waje da ministocin da suka gaza tabuka abin kirki a aikinsu.
Hadimar shugaban Najeriyan tayi wannan bayani ne wajen buda wani taro da aka shiryawa jami’an gwamnatin tarayya a Akwa Ibom.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An shiryawa jami'an gwamnatin Tinubu bita
A ranar Laraba aka yi taro na musamman, aka nunawa wakilan ma’aikatun gwamnati yadda za a cin ma manufofin shugaban kasa.
Shugabar ta sashen CDCU ta ce Bola Ahmed Tinubu da gaske yake yi wajen cin ma nasara da sauke alkawuran da ya dauka kafin a zabe shi.
A jawabin da ta gabatar a garin Uyo, Hadiza Bala Usman tace jami’an da suke wakiltar gwamnati za su lura da cigaba da kalubalen ministoci.
Jawabin Hadiza Bala Usman a Uyo
"Dole mu fahimci shugaban kasa da gaske yake yi game da alkawuransa, kuma za a auna ayyukan ministoci"
"Sannan za a sauke ministoci idan ba suyi aiki da kyau ba.
"Dole ku fahimci cewa a matsayin jami’an da ke wakilatar ma’aikatu, ku ne kan gaba wajen bada rahoto da bibiyar cigaba tare da kawo kalubalen ministoci zuwa ga sashen CDCU."
- Hadiza Bala Usman
This Day ta rahoto tsohuwar shugabar ta NPA tana bada misali da ma’aikatar harkokin jiragen sama, tace za a rika jin ta-cewar fasinjoji.
Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume ya halarci taron kuma ya gabatar da jawabi ta bakin wakilinsa, Olusegun Adekunle.
Lasisin Hadiza Bala Usman
Kwanaki aka ji labari jami’ai suna kurdowa Aso Rock idan ana taro, daga nan aka bada umarni babu wanda zai shigo taron FEC sai da izini.
Baya ga ministoci, Hadiza Bala Usman, Bayo Onanuga, Hakeem Muri-Okunola da Damilotun Aderemi kurum ake son gani a wannan zama.
Asali: Legit.ng