A Jawabin Shiga 2024, Shugaba Tinubu Ya Bayyana Ministoci da Hadiman da Zai Kora

A Jawabin Shiga 2024, Shugaba Tinubu Ya Bayyana Ministoci da Hadiman da Zai Kora

  • Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da jawabi ga daukacin mutanen Najeriya a kan sabuwar shekara da aka shiga
  • A jawabin, shugaban kasar ya jaddada barazanar da ya taba yi wa wadanda ya ba mukamai a gwamnatinsa
  • Tinubu ya ce za a rika auna kokarin da masu rike da kujerun gwamnati su ke yi, ba zai yarda da gazawa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Lagos - A ranar 1 ga watan Junairu, 2024, Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da jawabin shiga sabuwar shekara a Najeriya.

Jawabin Mai girma shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabo kalubalen da aka fuskanta a bara da kokarin da ake yi a yanzu.

Bola Tinubu
Bola Tinubu a gaban Ministoci da jami'an gwamnati Hoto: @officialABAT, @Dolusegun16
Asali: Twitter

The Nation ta ce shugaban kasar ya nanatawa wadanda ya ba mukamai cewa ba zai yarda da gazawa da rashin aiki ba.

Kara karanta wannan

2024: Abubuwa 10 da Tinubu ya fadawa Najeriya a jawabin shiga sabuwar shekara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ga wadanda aka ba aiki, Tinubu ya fadawa ‘yan Najeriya dole su sauke nauyin da ke wuyansu kamar yadda ake bukata.

Ba wannan ne karon farko da aka fadawa ministocin ana duba kwazonsu a karkashin ofishin Hadiza Bala Usman ba.

Tinubu yana so talaka ya samu sa'ida

Shugaban da aka rantsar a karshen watan Mayun 2023 ya ce yana so kowane mutumin kasar ya ji tasirin mulkinsa.

Jawabin ya ce tsare-tsaren gwamnati za su bada karfi ga talakawa da marasa galihu, kuma ba za a manta da ma’aikata ba.

Saboda haka ne shugaban Najeriyan ya yi alkawari za a kawo sabon tsarin albashi a shekarar 2024 la'akari da tsadar rayuwa.

Su wanene Bola Tinubu zai kora?

"Na yi rantsuwa zan bautawa kasar nan kuma in yi bakin kokarina a ko yaushe.

Kara karanta wannan

Atiku ya fadi matsala 1 da ta wajaba Shugaba Tinubu ya shawo kan ta a shekarar 2024

Kamar yadda na fada, babu wani uzurin rashin aikin da za a karba daga wadanda na ba mukamai.
Mun tsaida wasu ma’aunai domin yin gwaji. A cikin farkon sabuwar shekarar nan.
Ministoci da shugabannin hukumomin da za a cigaba da tafiya da su a gwamnatin nan da nake jagoranta za su cigaba da nuna kan su."

- Bola Tinubu

2024: Jawabin Bola Ahmed Tinubu

Labari da-dumi ya zo cewa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da jawabin shiga sabuwar shekarar 2024, ya yi maganar manufofinsa.

A cikin matakai mazu zafi da Shugaban Najeriyan ya ce ya dauka akwai cire tallafin fetur da na kudin ketare da ya jawo wayyo Allah.

Asali: Legit.ng

Online view pixel