Ana Fargabar Rayuka da Dama Sun Salwanta a Wani Sabon Rikicin da Ya Barke a Jihar Arewa
- Wani sabon rikici da ya ɓarke a jihar Plateau ya jawo an shiga fargabar rasa rayukan mutane da dama
- Rikicin dai ya auku ne a yankin Sabongari da ke a ƙaramar hukumar Mangu ta jihar wacce ke fama da rikice-rikice
- Jami'an tsaro sun tabbatar da aukuwar lamarin amma ba su bayyana adadin mutanen da suka rasa ransu ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Plateau - Ana fargabar an kashe mutane da dama tare da ƙona gidaje, coci da masallaci a yankin Sabongari da ke ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Filato a wani sabon rikici.
Wani ganau ba jiyau ba, Pansak Lazarus, wanda mazaunin yankin da lamarin ya faru ne, ya bayyana cewa ba za a iya tantance adadin waɗanda suka mutu ba kawo yanzu, cewar rahoton Leadership.
An kashe rayuka sama da 30 yayin da kashe-kashen bayin Allah ya ci gaba da safiyar nan a jihar Arewa
A kalamansa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ba zan iya ba ku ainihin adadin mutanen da aka kashe ba, amma an kashe da yawa. Sama da gidaje 15 ne aka ƙona tare da lalata shaguna da dama."
Me hukumomi suka ce kan lamarin?
A halin da ake ciki, kakakin rundunar ƴan sandan jihar, DSP Alfred Alabo, wanda ya zanta da manema labarai, ya yi kira da a kwantar da hankula, yana mai cewa ƴan sanda na bakin ƙoƙarinsu.
Hakazalika, jami’in yaɗa labarai na rundunar tsaro ta Operation Save Haven (OPSH), Kyaftin James Oya shi ma ya tabbatar da faruwar harin amma ya ƙi bayar da alƙaluman waɗanda suka mutu.
Ya bayyana cewa an tura dakarun OPSH zuwa yankin da abin ya shafa da nufin shawo kan lamarin, inda ya ƙara da cewa ƙura ta lafa yanzu.
Dan majalisa ya tabbatar da faruwar lamarin
Jaridar The Punch ta rahoto cewa tsohon ɗan majalisar da ke wakiltar Mangu ta Kudu, Bala Fwangyi, ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Tun da farko gwamnan jihar Plateau Caleb Mutfwang ya sanya dokar hana fita ta sa'o'i 24 a ƙaramar hukumar Mangu da ke jihar nan take sakamakon taɓarɓarewar tsaro a yankin.
Mutfwang Ya Faɗi Masu Taimakawa Ƴan Bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya bayyana masu taimakon ƴan bindiga a.jihar.
Gwamna Mutfwang ya bayyana cewa daga cikin jami'an tsaro akwai wasu gurɓatattu da ke ba ƴan bindiga bayanai.
Asali: Legit.ng