Yan bindiga sun kashe shugaban makarantar sakandare a Kaduna don ya ki yarda su tafi da shi

Yan bindiga sun kashe shugaban makarantar sakandare a Kaduna don ya ki yarda su tafi da shi

  • Rahotanni sun bayyana cewa'yan bindiga sun kashe wani shugaban makarantar sakandare a karamar hukumar Chukun da ke Kaduna
  • Sanata Shehu Sani ya sanar da kashe malamin, kuma ya ce 'yan bindigar sun yi nasarar tafiya da mata biyu a yayin farmakin
  • An ruwaito cewa malamin ya nunawa 'yan bindigar turjiya a lokacin da suka yi kokarin tafiya da shi, hakan ya sa suka kashe shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kaduna - Yan bindiga sun kashe wani Mallam Idris Abu Sufyan, shugaban makarantar sakandare (GSS) Kuriga, karamar hukumar Chukun da ke jihar Kaduna.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigar sun kashe malamin ne a ranar Juma'a a lokacin da suka yi kokarin sace shi amma ya ki yarda.

Kara karanta wannan

Basaraken Abuja da aka yi garkuwa da shi a 2023 ya kubuta, an biya naira miliyan 8 kudin fansa

Yan bindiga sun kashe shugaban makaranta a Kaduna
Kaduna: Yan bindiga sun kashe shugaban makaranta saboda ya yi masu turjiya. Hoto: @ShehuSani
Asali: Twitter

Dalilin da ya sa 'yan bindigar suka kashe Mallam Idris

Yan bindigar sun nuna tsantsar rashin imaninsu, kuma sun yi awon gaba da mata biyu a yayin farmakin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shehu Sani, tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter a ranar Asabar.

A cewar Sanata Sani, Mallam Sufyanu ya rasa rayuwarsa ne a yayin da ya ki yarda 'yan bindigar su tafi da shi.

Sanata Shehu Sani ya ba da labari

Tsohon sanatan ya wallafa cewa:

"Yan bindiga sun kashe Mallam Idris Abu Sufyan, shugaban makarantar sakandare (GSS) Kuriga, karamar hukumar Chukun, a jihar Kaduna.
"Sun kashe malamin ne a lokacin da ya nuna masu turjiya da suka yi kokarin tafiya da shi. Sai dai sun yi nasarar tafiya da mata biyu. Allah ya jikansa da Rahama. Ameen."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan sanda sun ceto wani mutum da aka sace a Abuja, an kama mai garkuwan

Ga abinda ya rubuta a kasa:

Yan bindiga sun tsare tsohon shugaban makaranta a Kaduna

A wani labarin kuma, Sanata Sani a ranar Talatar makon da ta gabata ya bada labarin wani tsohon shugaban makaranta da masu garkuwa suka tsare shi bayan ya kai masu kudin fansar wani.

Shehu Sani ya ce kwanan malamin uku kenan a hannunsu (a ranar da ya yi rubutun), kuma sun kira iyalansa, sun nemi a kai masu kudin fansa kafin su sako shi.

Sani ya ce lamarin ya faru ne a wani kauyen Birnin Gwari da ke jihar Kaduna, yankin da jama'ar cikinsa suka juma suna fama da hare-haren'yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel