Hadda Da Karatun Al-Kurani Mai Girma Yana Taimakawa Gyara Kwakwalwa, Gwamna Abdulrazaq

Hadda Da Karatun Al-Kurani Mai Girma Yana Taimakawa Gyara Kwakwalwa, Gwamna Abdulrazaq

  • Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya nemi al'ummar Musulmi da su dage da karatun Alkur'ani da haddarsa
  • Gwamna AbdulRazaq ya ce hadda da karatun Alkur'ani na taimakawa matuka wajen gyara kwakwalwa musamman ga matasa
  • Wani malamin addini da ya zanta da Legit Hausa, ya koka kan yadda matasa ke daina zuwa makarantar Islamiyya da zaran sun shiga sakandare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kwara - Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara, ya ce hadda da kuma karatun Alkur’ani mai girma na taimakawa matuka wajen gyara kwakwalwa a wajen masu karatu musamman matasa.

Ya kuma bukaci al’ummar musulmi da su tabbata suna yawaita karantawa tare da haddar littafin mai tsarki.

Kara karanta wannan

An kama ciyaman din PDP da wasu mutane 2 kan safarar bindigu a Zamfara

Karatun Al-Kur'ani tare da haddar sa na saita kwakwalwa
Karatun Al-Kur'ani tare da haddar sa na saita kwakwalwa, in ji Gwamna Abdulrazaq. Hoto: @RealAARahman, Getty Images
Asali: Getty Images

Gwamnan ya samu wakilcin Farfesa Mamman Saba Jibril

Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a ranar Lahadi a wajen rufe gasar Alkur’ani da Hadisi da ofishin jakadancin Saudiyya da ke Abuja da cibiyar nazarin da’awah da bincike ta As-Sunnah suka shirya a Ilorin, Jihar Kwara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar Farfesa Mamman Saba Jibril, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Jerin zakarun gasar Al-Kur'ani da Hadisi a ranar

Tribune Online ta ruwaito cewa zakarun masu saukar sun hada da Abdulrahman Ismail, Ahmad Abdulsalam, Abdullateef Zakariyah, Khadijah Ajijolakewu da Zainab AbdulGafar.

Sauran sun hada da Naeem Abdulsalam Usman Ayinde, Kamaldeen Suleiman da Abdulmajeed Abdullateef, Muslimah Abdullateef da Aisah Abdulrahman.

Sauran su ne Ahmad Abdulazeez, Sofiyullahi Murtadha, Maryam Abdulkareem, Maiyaki Muktar, Salimah Abubakar, Zainab Abubakar da Ali Muhammad.

Kiran Gwamna AbdulRazaq ga al'ummar Musulmi

Kara karanta wannan

Maza gabanku: Dakarun sojoji sun buɗe wa ƴan bindiga wuta, sun kashe da yawa a jihar arewa

Gwamnan ya ce ya zama wajibi ga Musulmi musamman matasa su ci gaba da neman ilimin Alkur’ani da Hadisi, gami da haddace su don ciyar da addinin Musulunci gaba.

Malam AbdulRazaq ya bayyana littafin mai tsarki a matsayin tushe na ilimin duk wani ilimi kuma ya nemi daliban da su sadaukar da kansu wajen karantawa da kuma nazarinsa akai-akai.

Me yasa yara da sun shiga sakandare suke daina zuwa Islamiyya?

Wani Mallam Abdulrahman, shugaban makarantar Islamiyya ta Makera, Funtua da ke jihar Katsina, ya koka kan yadda matasa ke daina zuwa Islamiyya da zaran sun shiga makarantar sakandare.

Mallam Abdulrahman, a zantawarsa da Legit Hausa ya ce akwai sakacin iyaye sosai akan wannan lamarin, wanda ya kira da 'fifita karatun zamani akan na addini."

Ya ce:

"Yaro idan yana makarantar sakandare, musamman ta kwana, to ya daina zuwa Islamiyya ke nan. Sau tari za ka ga sun koma zaman banza a cikin anguwanni.

Kara karanta wannan

Rundunar Soji ta tona asirin mutum 2 da ƙarin wasu abubuwa da suka jawo kashe-kashe a Filato

"Kuma abin bakin cikin, iyayensu suna kallon su ba tare da sun tsawatar masu ba. Yaro yakan samu damar yin karatun addini ne idan yana karami, amma da ya girma, ba shi da lokaci."

Shugaban makarantar da ya ke tsokaci kan abinda Gwamna AbdulRazaq ya ce game da muhimmancin haddar Al-Kur'ani mai girma, ya ce ba ko tantama, shiriya na zuwa a mu'amala da Al-Kur'ani.

Ya yi nuni da cewa daliban da ke zuwa na gaba gaba a makarantun jami'a, mafi akasari suna da kaifin haddar Al-Kur'ani, don hakan ya nemi matasa su rungumi ilimin addini.

Majalisar Dattijai za ta gurfanar da Wike a gabanta

A wani labarin, Sanata Ireti Kingibe ta ce Majalisar Dattijai za ta gana da ministan FCT Nyesom Wike da hukumomin tsaro don jin yadda aka bari rashin tsaro ya yi kamari a babban birnin tarayya Abuja.

A 'yan kwanakin nan 'yan bindiga musamman masu garkuwa da mutane sun matsawa mazauna Abuja da kai hare-hare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.