Yanzu-yanzu: Za a cigaba da bincike a kan Magu a yau Talata

Yanzu-yanzu: Za a cigaba da bincike a kan Magu a yau Talata

- Kwamitin da aka kafa domin bincike kan zarge zargen da ake yi wa Ibrahim Magu za ta cigaba da zamanta ranar Talata

- Tun a jiya Litinin ne kwamitin karkashin tsohon alkali kotun koli, Ayo Salami ta gayyaci Ibrahim Magu

- Rahotanni sun bayyana cewa Mr Magu bai koma gidansa ya kwana ba duba da cewa kwamitin ba ta kammala tamboyoyin da ta ke masa ba

Kwamitin shugaban kasa mai mutane bakwai da ke bincike a kan tuhume-tuhumen da ake yi wa shugaban riko na hukumar yaki da rashawa EFCC za ta cigaba da zamanta karfe 10 na safe.

Tsohon alkalin kotun daukaka kara mai murabus, Mr Ayo Salami da wasu jami'an gwamnati daga wasu hukumomi ne za su jagoranci kwamitin.

An dai lissafa laifuka kimanin 22 da ake tuhumar Magu da aikatawa kamar yadda kafar TVC ta ruwaito.

Yanzu-yanzu: Za a cigaba da bincike a kan Magu a yau Talata
Yanzu-yanzu: Za a cigaba da bincike a kan Magu a yau Talata. Hoto daga TVC
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An kama matar kwamandan Boko Haram (Hoto)

Amma lauyoyinsa sun ce sun shirya da hujojin da za su kare shi inda suka ce tun farko ma babu wata dalilin da zai sa a tsare shi.

A baya Legit.ng ta wallafa cewa Oluwatoyin Ojaomo, lauyan shugaban riko na hukumar yaki da rashawa ta EFCC, Ibrahim Magu, ya ce masu son ganin maigidansa sun fi annobar korona karfi.

Ojaomo ya bayyana hakan ne a cikin shirin gidan talabijin na Channels yayin da ya ke mayar da martani a kan gayyatar da wani kwamitin shugaban kasa ya yi wa Magu a yau, Litinin.

Lauyan ya ce kwamitin bincike ya gayyaci Magu ne domin ya yi bayani a kan gibin da aka samu a adadin kudin da EFCC ta saka a aljihun gwamnati da kuma wanda Magu ya sanar a bainar jama'a.

A cewar Lauyan, adadin kudin da Magu ya mayar aljihu gwamnati sun zarce adadin kudin da ya sanar EFCC ta kwace.

"Idan kana yaki da cin hanci, ka sani cewa cin hanci zai yakeka, cin hanci ya yi karfi sosai, ma su cin hanci sun yi karfi, sun fi annobar korona karfi.

"Yanzu ku duba abinda yake faruwa, sakamakon a yabawa Magu, manyan mutanen da suka yi karfi saboda cin hanci suna kokarin bata ma sa suna ta hanyar amfani da kafafen yada labaran da su ka mallaka," a cewar Ojaomo.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel