Shahararren Farfesa a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya Ya Na Shekaru 94 a Duniya

Shahararren Farfesa a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya Ya Na Shekaru 94 a Duniya

  • Allah ya karbi rayuwar shahararren marubuci, Farfesa Okoro Anezionwu a jihar Enugu ya na da shekaru 94
  • Dan marigayin, Chukwuma Anezionwu shi ya tabbatar da hakan a yau Asabar 20 ga watan Janairu a jihar Enugu
  • Daga cikin littattafan da ya wallafa akwai ‘One Week’ da ‘The Village Headmaster’ da ‘One Trouble’ da sauransu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Enugu – Sahahararren mawallafin littattafai a Najeriya, Farfesa Anezionwu Okoro ya riga mu gidan gaskiya.

Dan marigayin, Chukwuma Anezionwu shi ya tabbatar da hakan a jiya Asabar 20 ga watan Janairu a jihar Enugu.

Fitaccen Farfesa a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya
Farfesa Okoro ya rasu da safiyar ranar Asabar a Enugu. Hoto; Anezionwu Okoro.
Asali: Facebook

Yaushe marigayin ya rasu a Enugu?

Marigayin wanda ya wallafa sanannun littattafai da dama ya rasu ne ya na da shekaru 94 a duniya, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Gyadar dogo: Mutanen da suka sha da kyar da aka kifar da Gwamnatin Najeriya a 1966

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin littattafan da ya wallafa akwai ‘One Week’ da ‘The Village Headmaster’ da ‘One Trouble’ da sauransu.

Yayin sanar da mutuwar Farfesan, Chukwuma ya ce mahaifin nasa ya mutu cikin aminci a cikin barcinsa da safiyar ranar Asabar 20 ga watan Janairu.

Ya ce:

“Ya yi fama da jinya na wani lokaci, ya mutu da misalin karfe 4:00 na asuba, tabbas za mu yi rashin mahaifi mai kulawa.”

Waye ne Farfesa Okoro a Najeriya?

An haifi Anezi Okoro a ranar 17 ga Mayun shekarar 1929 a yankin Arondizuogu da ke jihar Imo, cewar Tribune.

Okoro ya yi makarantar firamare a Kwalejin Methodist da ke Uzuakoli da ke jihar Abia a Kudu maso Gabshin Najeriya.

Sannan marigayin ya koyar a Jami’ar koyar da karatun likitanci a Georgia a watan Agustan shekarar 1987.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun koma fada da juna, an tarwatsa yaran mashahurin ‘dan ta’adda

Daga bisani marigayin ya koma Jami’ar Minnesota da ke Minneapolis a shekarar 1988 da kuma Jami’ar King Faisal, a Damman da ke Saudiyya daga 1989 zuwa 1995.

Farfesa Kperogi ya caccaki Tinubu

A wani labarin, Farfesa Farouk Kperogi ya bayyana kuskuren da Bola Tinubu ya yi kan takardun makaranta.

Kperogi ya ce Tinubu ya yi ganganci da ya mika takardun da ba a tantance a Jami'ar Chicago ga hukumar zabe mai zaman kanta, INEC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel