Dakarun Sojoji Sun Sheke Manyan Kwamandojin Yan Ta'adda 3, Sun Ceto Mutum 27 da Aka Sace

Dakarun Sojoji Sun Sheke Manyan Kwamandojin Yan Ta'adda 3, Sun Ceto Mutum 27 da Aka Sace

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasara a yakin da suke yi da ƴan ta'adda masu tayar da ƙayar baya a ƙasar nan
  • Haziƙan sojojin sun halaka manyan kwamandojin ƙungiyar ƴan ta'adda ISWAP guda uku tare da mayaƙa 43 a jihar Borno
  • Sojojin sun kuma samu nasarar ceto mutum 27 da ƴan ta'adda suka yi garkuwa da su ba tare da son ransu ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hedikwatar tsaro (DHQ) ta ce dakarun sojin Najeriya sun halaka wasu manyan kwamandojin ƙungiyar ƴan ta'addan ISWAP guda uku a Borno.

Daraktan yaɗa labarai na DHQ, Edward Buba, wanda ya yi magana a Abuja ranar Juma’a, yayin da yake bayar da rahoton mako-mako na ayyukan rundunar a faɗin ƙasar nan, ya ce sojojin sun kuma kashe ƴan ta’adda 43, cewar rahoton TheCable.

Kara karanta wannan

Hukuncin Kotun Koli: Dan takarar PDP ya aike da sako mai muhimmanci bayan rigima ta barke a Arewa

Sojoji sun sheke kwamandojin ISWAP
Dakarun sojoji sun sheke kwamandojin ISWAP 3 a Borno Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Twitter

Buba ya danganta nasarar da sojojin suka samu a kan ɓangaren sojojin sama na Operation Hadin Kai, inda suka kai harin a ranar 10 ga watan Janairu, rahoton Daily Post ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana kwamandojin ƴan ta’addan da aka kashe a matsayin Abou Maimuna, Abou Zahra, da Kwamanda Saleh, inda ya ce su da mayaƙansu na cikin kwale-kwale kafin a kai musu farmaki da halaka su.

Sojojin sun kuma cafƙe ƴan ta'adda

A cewar kakakin hedikwatar tsaron, an kuma cafke ƴan ta’adda 76 yayin da aka kuɓutar da mutum 27 da aka yi garkuwa da su.

Ya ƙara da cewa an ƙwato makamai iri-iri guda 81, alburusai iri-iri guda 2,150, tsabar kuɗi N1m, da sauran kayayyaki a yayin aikin.

"Rundunar sojoji za su ci gaba da yin la'akari da barazanar da ake fuskanta ta ƙungiyoyin masu garkuwa da ƙungiyoyin ƴan ta'adda a faɗin ƙasar nan."

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun ragargaji yan bindiga, sun ceto mutanen da suka sace a jihar Arewa

Sojoji Sun Sheƙe Kwamandojin Ƴan Ta'adda

A wani labarin kuma kun ji cewa hedikwatar tsaro ta ƙasa ta tabbatar da kashe wasu fitattun kwamandojin ƴan ta'adda huɗu a hare-haren da aka kai ta sama cikin mako guda.

Ƴan ta'addan da suka baƙunci lahira sun haɗa da Haro Dan Muhammadu, Ali Alhaji Alheri wanda aka fi sani da Kachalla Ali Kawaje da Machika.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng