“Na Kasa Numfashi”: Matar Aure Ta Bankado Wani Boyayyen Sirrin Mijinta Shekaru 4 Bayan Aurensu

“Na Kasa Numfashi”: Matar Aure Ta Bankado Wani Boyayyen Sirrin Mijinta Shekaru 4 Bayan Aurensu

  • Wata mata yar Najeriya ta koka a soshiyal midiya bayan ta gano cewa mijinta na da wani dan tare da wata mata da daban
  • Matar da ta karaya ta bayyana cewa danginsa na sane da lamarin sannan ta bayyana yadda suka dunga yi mata rufa-rufa
  • Masu amfani da soshiyal midiya sun tausaya ma matar sannan sun bata shawara kan yadda za ta tafiyar da al'amarin

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wata matar aure mai suna Onyinye Okoli, ta koka a soshiyal midiya bayan gano cewa mijinta na shekaru hudu da haifi wani dan a waje.

Wata mai amfani da dandalin Facebook, Maria Ude Nwachi ce ta wallafa labarin kuma tuni ya haddasa cece-kuce a tsakanin jama'a.

Kara karanta wannan

An yi wa shahararriyar mawakiyar Najeriya, Tiwa Savage, fashi a Landan

Matar ta gano mijin na da wani dan a waje
An yi amfani da hoton don misali ne kawai Hoto: Per-Anders Pettersson, Thomas Imo
Asali: Getty Images

A cewar Onyinye, matar da ya yi wa ciki ta haihu ta kasance wacce yan uwansa suka gabatar mata da ita a matsayin kanwarsa da suke uba daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Onyinye wacce ta karaya gaba daya ta bayyana a dandalin soshiyal midiya cewa bata iya numfasawa.

Ga cikakken wallafarta a kasa:

"Auren shekaru 4. A yau na gano cewa mijina na da yar dan watanni 2 tare da wata mata wacce shi da danginsa suka gabatar mun da ita a matsayin kanwarsa da suke uba daya. Na kasa numfasawa."

Mutane sun ba matar shawara

Gold Ogbonnia ta ce:

"Muna addu'ar Allah yasa ranar da za mu gano abun da abokan zamanmu ke boye mana kada ya daidaita mu gaba daya. Yar'uwata ki numfasa sosai.
"Allah ya karfafa ki."

Ijehor Tonia ta ce:

Kara karanta wannan

Budurwa ta koka bayan ta ci karo da shinkafa a cikin cincin din 'mitifie' da ta siya a Legas

"Gwanda ki numfasa yar'uwa. Ki hada kanki waje guda, ba sabon abu bane yadda kike ji a yanzu. Ba karshen ki ba kenan. Don haka ki numfasa sannan ki kasance cikin koshin lafiya."

Ifechukwu Juliet Onuigbo ta ce:

"Ki numfasa yar'uwa.
"Aikin gama ya gama.
"Ki kakkabe kanki ki ci gaba da rayuwarki."

Yayar amarya ta kasa ta tsare a wajen biki

A wani labari na daban, wani bidiyo ya nuno lokacin da ya yayar amarya ta hana wata yar biki yi wa kanwar tata ruwan liki.

Wata mai amfani da dandalin TikTok, @alagaomolayinke, ta jinjinawa yayar amaryar yayin da ta yada bidiyon.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng