Dirama Yayin da Yayar Amarya Ta Hana Wata Yi Mata Liki a Wajen Biki, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

Dirama Yayin da Yayar Amarya Ta Hana Wata Yi Mata Liki a Wajen Biki, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

  • Jama'a sun yi martani yayin da wani bidiyo ya nuno irin diramar da aka sha tsakanin yayar amarya da wata mata da ta halarci taron bikinsu
  • Yayin da suke filin rawa, wata mata ta shiga sahun sauran mutane sannan ta yi kokarin yi wa amaryar liki
  • Yanayin yadda yayar amaryar ta yi wa matar da ke kokarin liki ba tare da wata manufa ba ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wani bidiyo ya nuno lokacin da ya yayar amarya ta hana wata yar biki yi wa kanwar tata ruwan liki.

Yayar amarya ta hana wata liki a wajen biki
Dirama Yayin da Yayar Amarya Ta Hana Wata Yi Mata Liki a Wajen Biki, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce Hoto: @alagaomolayinke
Asali: TikTok

Wata mai amfani da dandalin TikTok, @alagaomolayinke, ta jinjinawa yayar amaryar yayin da ta yada bidiyon.

Kara karanta wannan

"Na wahala da shi": Budurwa ta fashe da kuka yayin da saurayinta na shekaru 7 ya auri wata

"Kowace amarya na bukatar yar'uwa kamar wannan!!! Ki lika kudin a jaka ko a kasa!" ta rubuta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin bidiyon, mahalarta bikin sun kewaye amaryar. Wasu na yi mata liki amma dai yayar tata ta mayar da hankali ne kan mutum daya daga cikinsu.

Duk da turjewar da amaryar ta yi a tsanaki, ta sake ture hannun matar da ke likin.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

CHEEKA ta ce:

"Ha!!’ Da gangan take yin wannan sannan harda daukar kudin. Ya kamata amaryar ta sake duba wannan bangaren faaa. Yayarta ta yi kokari."

Bhadmus1812 ta ce:

"Na halarci wani biki a ranar Alhamis da ya gabata, wani mutumi na ta yi wa amaryar liki bayan ya gama yi mata liki, sai ya kuma daura hannunsa a kanta."

officialqueen289 ta ce:

Kara karanta wannan

Mata sun yi zanga-zanga kan kisan wata matar aure da mijinta ya yi a Yobe

"A nawa bikin babu wanda ya kai gareni kai tsaye saboda an ajiye manyan yan dambe biyu a gaba wadannan mugayen mutanen kauye."

Harewah ta ce:

"Ji fa wai amaryar na ce mata ta kwantar da hankalinta, idan da ta san hatsarin da take gareta daga gare shi."

Matashi ya ce mata 7 yake son mallaka

A wani labarin kuma, mun ji cewa wani matashi dan Najeriya mai suna Obafolarin, ya jinjinawa matansa biyu, Ayomide da Mayowa a dandalin soshiyal midiya.

A wani bidiyon TikTok, matashin mawakin yana ta wasa da su yayin da yake nunawa duniya yadda suke zamansu lafiya a gidan aurensu.

Asali: Legit.ng

Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel